Wani ya kashe kansa a harabar ofishin hukuma saboda tarar N215,000
Hankula sun tashi a harabar Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Ogun, TRACE, a ranar Litinin 20 ga watan Yuli bayan wani mutum mai suna Fatai Salami ya kashe kansa a harabar hukumar.
A cewar rahotanni, Jami'an TRACE sun kama direban Salami ne ranar Alhamis 16 ga watan Yuli a Abeokuta saboda ya saba dokokin dakile annobar cutar coronavirus a jihar.
An zargi cewa baya kiyaye dokar bayar da tazara a cikin motarsa kuma bai saka takunkumin rufe fuskarsa ba kamar yadda Linda Ikeji Blog ta ruwaito.

Asali: Twitter
An kwace motarsa aka tafi da ita harabar hukumar TRACE sannan aka ci shi tarar N215,000. Nan take ya kira mai gidansa, Mr Salami domin sanar da shi abinda ya faru.
Mr Salami ya iso harabar hukumar TRACE nan take inda har ya kwana a harabar hukumar yana rokon alfarma a saki motarsa da aka kama.
DUBA WANNAN: Muddin muna tare ba zan taɓa yin arziki a duniya ba - Matar aure ta garzaya kotu
Rahotanni sun ce Salami ya kawo N150,000 amma jamian hukumar ba su karba ba. Hakan yasa ya yi barazanar zai kashe kansa amma ba a kula shi ba. Daga nan ya sha maganin kashe kwari ya mutu.
Da ya ke tsokaci a kan lamarin, Kakakin hukumar TRACE, Babatunde Akinbiyi ya musanta cewa mutumin yana da mota kuma yace ba a ci tarar shi ba.
"Mutumin ba direban mota bane kuma bai mallaki mota ba. Mun ga shi ne kawai a wurin kuma da mutane suka bukaci ya tashi ya tafi sai ya ciro wani abu daga aljihunsa ya sha.
"Daga baya mun gano cewa abinda ya sha maganin kashe kwari ne. An garzaya da shi babban asibiti inda ya mutu a can. An kai wa 'Yan sanda rahoto," a cewar Akinbiyi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng