Ina yi wa Ministan harkokin waje fatan samun waraka cikin gaggawa - Buhari

Ina yi wa Ministan harkokin waje fatan samun waraka cikin gaggawa - Buhari

A jiya Lahadi da daddare, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi fatan samun sauki ga Ministansa na Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Geoffery Onyeama, wanda ya kamu da cutar korona.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce Buhari ya misalta ministan a matsayin wani babban ginshiƙi mai ƙarfi a gwamnatinsa.

Bisa la'akari da kasancewarsa dan kwamitin yaki da annobar korona na kasa, Buhari ya yabawa ministan dangane da kwazonsa a fagen yaki da cutar korona da kuma tabbatar da amincin 'yan Najeriya mazauna ketare.

Legit.ng ta ruwaito cewa, Geoffrey Onyeama, ministan harkokin wajen Najeriya, ya sanar da cewa ya kamu da cutar korona.

Ministan harkokin wajen Najeriya; Geoffery Onyeama
Ministan harkokin wajen Najeriya; Geoffery Onyeama
Asali: UGC

Onyeama ya sanar da hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuli tare da cewa yana kan hanyarsa ta zuwa cibiyar killacewa.

"Na yi gwajin cutar korona karo na hudu a jiya bayan alamun ciwon makogwaro, sai dai kuma abun bakin ciki shine ya bayyana ina dauke da cutar a wannan karon.

"Wannan ita ce rayuwa, ka yi nasara a nan, ka fadi a can. Ina hanyar zuwa cibiyar killacewa kuma ina addu'ar dacewa da mafificin alkhairi," ya wallafa.

KARANTA KUMA: Masu tireda sun yi zanga-zanga kan rushe musu rumfuna a bakin kasuwannin Kano

Minista Onyeama shi ne minista na farko da ya kamu da muguwar cutar a cikin 'yan majalisar zartarwa na gwamnatin shugaba Buhari.

Sai dai ana iya tuna cewa, cutar korona ce ta yi sanadiyar mutuwar tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.

Abba Kyari ya rasu ne sakamakon kamuwa da cutar Covid-19 wadda ya harbu da ita a karshen watan Maris da ya gabata bayan dawowa daga wata ziyarar aiki da ya kai a kasar Jamus.

Mai yankan kauna ta yi wa Marigayi Kyari lullubi a yayin da yake jinya a wani asibiti a jihar Legas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel