Masu tireda sun yi zanga-zanga kan rushe musu rumfuna a bakin kasuwannin Kano

Masu tireda sun yi zanga-zanga kan rushe musu rumfuna a bakin kasuwannin Kano

‘Yan tireda a kasuwar Sabongari sun nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira a matsayin zalunci yayin da Hukumar Kula da Sufuri ta Kano KAROTA ta rushe musu rumfuna da shaguna.

Kwanaki uku da suka gabata ne Hukumar KAROTA ta yi rusau a wasu manyan kasuwanni na jihar Kano inda ta rushe fiye da shaguna 500 da ke wuraren da suka saba ka'ida a kan tituna.

A yau Litinin, 'yan kasuwa da wasu al'ummar gari sun yi zanga-zanga ta nuna bacin rai dangane da wannan lamari da wasunsu ke kira a matsayin toshe musu hanyar cin abinci.

A wani faifan bidiyo da jaridar Daily Trust ta wallafa a shafinta na Twitter, ya hasko yadda wasu matasa ke zanga-zanga a bakin Kasuwar Singer daura da Kasuwar Sabon Gari.

Yadda aka yi rusau a Kasuwar Sabon Gari
Hakkin mallakar hoto; Daily Trust
Yadda aka yi rusau a Kasuwar Sabon Gari Hakkin mallakar hoto; Daily Trust
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi dan takaitaccen rikici tsakanin jami'an 'yan sanda da kuma wasu daga masu kasa kaya a gefen tituna a bakin kasuwar Sabon Gari.

Takaddamar ta auku ne a yayin da 'yan kasuwar ke gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadin matakin da Gwamnatin Kano ta dauka na haramta kasa kaya a gefen titin kasuwar.

Kwanaki uku da suka gabata ne gidan Rediyon Freedom ya ruwaito cewa, Hukumar KAROTA ta sanar da kammala duk wani shiri na kai simame wuraren da 'yan kasuwa ke kasa a kan tituna da wuraren da basu dace ba.

KARANTA KUMA: Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban hafsan sojin kasa, Buratai

Shugaban Hukumar KAROTA, Alhaji Baffa Babba Dan Agundi, shi ne ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyarar gani da ido wuraren da aiki zai biyo takansu tun a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli.

A yayin da yake zantawa da manema labarai, Dan Agundi ya ce akwai fiye da shaguna dubu biyar da aka bari kara zube a gefen tituna da bakin kasuwanni a birnin Kano da kewaye.

Daga cikin kasuwannin da shugaban KAROTA ya wassafa sun hadar da ta Sabuwar Tasha, Kwanar Ungogo, Unguwar Nassarawa, Yankin Masana'antu da kuma ta Sabon Gari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel