Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban hafsan sojin kasa, Buratai
A yanzu dinnan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya shiga wata ganawa ta sirri tare da shugaban hafsan sojin kasa na Najeriya, Lt. Gen. Tukur Buratai, a fadar Aso Rock.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, babu wani rahato da ya fito dangane da dalilin wannan ganawa da shugaban kasar yake yi tare da shugaban dakarun sojin.
Sai dai akwai yiwuwar wannan ganawa tana da nasaba da al'amuran gudanarwa na dakarun soji wajen tabbatar da aminci a Arewa maso Gabas da kuma yankin Yammacin Arewa.
A baya bayan nan ne shugaba Buhari ya yi wata ganawa da shugabannin tsaro inda ya ja kunnensu tare da tsawata musu a kan kokarin da suke yi na sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Asali: Twitter
A cewar shugaban, dole ne sai shugabannin tsaro sun kara kokarin da suke yi wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake fuskanta a kasar.
KARANTA KUMA: Harin da 'yan bindiga suka kai mana a Katsina dakaru 3 ne kawai suka mutu - Rundunar Soji
Ya nuna rashin gamsuwarsa da rashin hadin kai a tsakanin shugabannin tsaro, lamarin da ya sanya ya yi musu gargadi kan yin aiki tare don kawo karshen kalubalen tsaro da ke addabar kasar.
Wannan kalami na shugaban sun kasance kalamai mafiya kaushi game da salon shugabanin na tsaro a daidai lokacin da yanayin tsaro ke kara muni a Arewacin Najeriya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng