Binciken badakala: Shugaban hukumar NDDC ya tayar da bori, ya fadi 'warwas' a gaban kwamiti

Binciken badakala: Shugaban hukumar NDDC ya tayar da bori, ya fadi 'warwas' a gaban kwamiti

Mista Kemebradikumo Pondei, mukaddashin shugaban hukumar kula da cigaban yankin Neja-Delta (NDDC), ya fadi kasa 'warwas' yayin da yake daukan rantsuwa a gaban kwamitin binciken badakalar biliyoyi a NDDC.

A ranar Litinin ne Mista Pondei tare da ministan yankin Neja-Delta, Sanata Godswill Akpabio, suka bayyana a gaban kwamitin domin bayar da bayanai da kuma kare kansu daga badakalar da ake zargin an tafka a NDDC.

Binciken badakala: Shugaban hukumar NDDC ya tayar da bori, fadi 'warwas' a gaban kwamiti
Shugaban hukumar NDDC ya tayar da bori
Asali: Twitter

Binciken badakala: Shugaban hukumar NDDC ya tayar da bori, fadi 'warwas' a gaban kwamiti
Shugaban hukumar NDDC ya tayar da bori a gaban kwamiti
Asali: Twitter

Kwamitin bincike ya yi zargin cewa Mista Pondei ya kashe kudaden NDDC da yawansu ya kai biliyan N40 ba tare da saka kudin a cikin kasafi ba.

A yayin da Mista Pondei ya mike domin daukar rantsuwa gabanin fara amsa tambayoyi da kuma kare kansa daga zargin da ake yi ma sa, sai kawai ya fara bori, kamar mai aljanu, kafin daga bisani ya yanke jiki ya fadi.

Kafin faruwar hakan, Legit.ng ta wallafa rahoton cewa shugaban kwamitin majalisar wakilai da ke binciken badakalar kudi a hukumar kula da cigaban yakin Neja - Delta (NDDC), Honarabul Olabunmi Tunji - Ojo, ya sauka daga mukaminsa.

DUBA WANNAN: Sabon harin 'yan bindiga: An kashe mutane 19, an raunata 30 a Kaduna

A makon jiya ne kwamitin majalisar ya fara gayyatar tsofin shugabanni da ma su ci yanzu a hukumar NDDC domin amsa tambayoyi a kan badakalar da ake zargin ana tafkawa a hukumar.

Honarabul Tunji - Ojo, ya sanar da yin murabus dinsa ne ranar Litinin yayin zaman kwamitin domin cigaba da gudanar da binciken badakala a hukumar NDDC.

A ranar Alhamis din makon jiya ne Pondei ya jagoranci mukarrabansa wajen ficewa daga dakin da kwamitin majalisa ke yi ma sa tambayoyi a kan zargin badakala a hukumar NDDC.

Murabus din dan majalisar ba zata rasa nasaba da zarginsa da cin hanci da Mista Pondei ya yi ba a makon jiya.

Da ya ke bayyana dalilinsa na ficewa daga wurin zaman kwamitin bincike da majalisa ta kafa, Mista Pondei ya bayyana cewa ba zai yi magana a gaban kwamitin da ake zargin shugabansa da cin hanci ba.

Sauran mambobin kwamitin sun bayyana amincewarsu da shugabancin Honarabul Tuni - Oyo. Kazalika, sun bukaci Mista Pondei da ministan yankin Neja - Delta, Sanata Godswill Akpabio, su bayyana a gaban kwamitin ranar Litinin, 20 ga watan Yuli.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel