Buhari ya tsawaita wa'adin shugaban Hukumar NSCDC

Buhari ya tsawaita wa'adin shugaban Hukumar NSCDC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da tsawaita wa'adin Kwamandan Rundunar Tsaron Al'umma ta Najeriya (NSCDC), Abdullahi Gana Muhammadu.

Shugaban kasar ya amince a tsawaita wa'adin shugaban hukumar NSCDC daga yanzu har zuwa tsawon watanni shida.

Mai magana da yawun Kwamanda Janar Gana, Ekunola Gbenga, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi yayin ganawa da manema labarai.

Sabanin rade-radin da ke yaduwa na cewa Buhari ya sabunta nadin mukamin shugaban na NSCDC na tsawon shekaru biyar da zai kare a ranar 17 ga watan Yulin 2020, Mista Gbenga yace kanzon kurege ne.

Mista Gbenga ya ce wannan zantuttuka ne kawai na shaci fadi da wasu ke kirkira domin su haifar da matsala a hukumar NSCDC.

Shugaban Hukumar NSCDC; Abdullahi Gana Muhammad
Hoto daga Pulse.ng
Shugaban Hukumar NSCDC; Abdullahi Gana Muhammad Hoto daga Pulse.ng
Asali: UGC

"Ya kirayi al'umma da su yi watsi da wannan jita-jita da babu abinda za ta tsinana face ta kai su kuma ta baro".

Ya ce Buhari ya tsawaita wa'adin shugaban hukumar NSCDC ne ta hannun Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, kuma za ta fara aiki ne daga ranar 17 ga watan Yulin 2020.

KARANTA KUMA: SERAP ta nemi Buhari ya dakatar da Akpabio kuma ya kafa kwamitin bincikarsa

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, an tsawaita wa'adin Kwamandan na NSCDC bisa la'akari da kwazon aiki da kuma rawar da ya taka wajen bunkasa harkokin gudanarwa da kuma inganci a hukumar.

Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar ASUU ta goyi bayan shawarar da Gwamnatin Tarayya ta yanke na dakatar da daliban aji shida daga zana jarrabawar WAEC da aka shirya farawa a ranar 4 ga watan Agusta.

Kungiyar Malaman Jami'o'in ta shawarci gwamnatin tarayya da ta bar makarantu a rufe har zuwa shekarar 2021 don tabbatar da ingantaccen shiri kafin a sake buɗe su.

ASUU ta buga misali da hukuncin da gwamnatin kasar Kenya ta yanke na cewa kafatanin makarantu a kasar za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai shekara mai zuwa.

A wata hira da shugaban ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi ya yi da manema labarai na jaridar The Punch a ranar Lahadi, ya ce kar a kuskura a yi sakaci da lafiyar dalibai.

Farfesa Ogunyemi ya ce kada a sake a buɗe makarantu har sai gwamnatin tarayya ta samu yarjewa ta iyayen yara kuma sun nuna amincewarsu a kan hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel