SERAP ta nemi Buhari ya dakatar da Akpabio kuma ya kafa kwamitin bincikarsa

SERAP ta nemi Buhari ya dakatar da Akpabio kuma ya kafa kwamitin bincikarsa

Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da cin hanci da rashawa, ta kirayi shugaban Muhammadu Buhari da ya kafa wani kwamiti na domin gudanar da bincike kan badakalar rashawa a hukumar raya Neja Delta.

Kungiyar mai zaman kanta, ta kuma nemi shugaban kasar da ya gaggauta dakatar da Ministansa na Harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio da duk wasu da ake zargi da badakar rashawa har sai an gudanar da bincike a kansu.

SERAP ta ce akwai muhimmiyar bukata a kafa kwamitin domin aiwatar da binciken diddigi a hukumar NDDC da kuma ma'aikatar kula da harkokin Neja Delta.

Wannan kira yana kunshe ne cikin wata budaddiyar wasika mai kwanan watan ranar 18 ga Yuni, wadda mataimakin darektan Kungiyar SERAP, Kolawole Oluwadare ya sanya wa hannu.

SERAP ta bayyana muradin a yi bincike kan ikirarin da Hukumar NDDC ta yi na cewa ta kashe naira biliyan 81.5 wajen harkokinta na gudanarwa daga watan Janairu zuwa Yulin 2020.

Godswill Akpabio
Hoto daga Jaridar Vanguard
Godswill Akpabio Hoto daga Jaridar Vanguard
Asali: UGC

Legit.ng ta ruwaito cewa, kwamitin da majalisar tarayya ta kafa don bincike kan badakalar da aka tafka a hukumar NDDC ya bukaci Ministan Neja Delta da ya bayyana gabansa kafin karfe 11 na safiyar ranar Litinin.

A wani labarin makamancin wannan kuwa, Tsohuwar shugabar hukumar NDDC, Joy Nunieh, ta fayyace gaskiya gaban majalisar tarayyar kan binciken badakalar da aka tafka a hukumar NDDC.

Daga ranar Alhamis ne binciken da ake yi na badakalar hukumar NDDC ya kara daukan zafi inda jami'an rundunar 'yan sanda suka mamaye gidan Nunieh da ke Fatakwal.

KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun yi wa sojojin Najeriya kwanton bauna, sun kashe 16 a Katsina

A ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, 2020, shugabar hukumar NDDC da aka sallama daga aiki, ta yi alkawarin cewa ‘yan Najeriya za su ji karin bayani kan ta’adin da aka yi a gwamnati.

Dakta Nunieh ta bayyana wannan ne yayin da ta ke tsakiyar rigima da Mista Akpabio da majalisar tarayya a kan badakalar da aka tafka a Hukumar NDDC.

Joy Nunieh ta yi jawabi ne a fadar gwamnatin jihar Ribas bayan gwamna Nyesom Wike ya cece ta daga hannun ‘yan sanda. Ana zargin an yi yunkurin hana Nunieh hallara ne gaban majalisar.

Jaridar Vanguard ta ce dakarun Mopol sun dura gidan Joy Nunieh da ke layin Herbert Macaulay a unguwar GRA, Fatakwal, a jihar ne da karfe 4:00 domin hana ta tafiya zuwa Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel