Coronavirus: Kar a buɗe makarantu har sai 2021 - ASUU
- Kungiyar ASUU ta bada shawarar a dakatar da zana jarrabawar kammala karantun sakandire ta WAEC a bana
- Shugaban ASUU na kasa ya goyi bayan hukuncin da gwamnatin tarayya ta yanke a kan kin buɗe makarantu
- Biodun Ogunyemi ya ce ya kamata makarantu su ci gaba da kasancewa a rufe har sai shekarar 2021
Kungiyar ASUU ta ce ta goyi bayan shawarar da Gwamnatin Tarayya ta yanke na dakatar da daliban aji shida daga zana jarrabawar WAEC da aka shirya farawa a ranar 4 ga watan Agusta.
Kungiyar Malaman Jami'o'in ta shawarci gwamnatin tarayya da ta bar makarantu a rufe har zuwa shekarar 2021 don tabbatar da ingantaccen shiri kafin a sake buɗe su.
ASUU ta buga misali da hukuncin da gwamnatin kasar Kenya ta yanke na cewa kafatanin makarantu a kasar za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai shekara mai zuwa.

Asali: UGC
A wata hira da shugaban ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi ya yi da manema labarai na jaridar The Punch a ranar Lahadi, ya ce kar a kuskura a yi sakaci da lafiyar dalibai.
Farfesa Ogunyemi ya ce kada a sake a buɗe makarantu har sai gwamnatin tarayya ta samu yarjewa ta iyayen yara kuma sun nuna amincewarsu a kan hakan.
KARANTA KUMA: Dokin zuciya: Bidiyon yadda mai Keke Napep ya dambace da jami'an FRSC a Edo
A makon nan ne gwamnatin tarayya ta zauna a kan teburin sulhu da hukumar shirya jarrabawar kammala karatun sakandire ta Yammacin Afrika (WAEC) domin sauya ranar da za a fara gudanar da jarrabawa a bana.
Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya kuma ce gwamnatin za ta tuntubi wasu kasashe uku masu zana jarrabawar WAEC domin a tsayar da sabuwar ranar fara gudanar da ita.
Nwajiuba ya bayyana hakan ne yayin sanar da cewa, an sanya wa makarantu wa'adi na tabbatar da sun cika duk wasu sharudan dakile yaduwar cutar korona daga yanzu zuwa ranar 29 ga watan Yuli.
Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamnatin Najeriya da hukumar WAEC sun cimma matsayar sauya ranar jarabawar ta bana.
A maimakon fara jarabawar a ranar 4 ga watan Augusta da ta sanar a baya, a yanzu za a fara gudanar da ita a ranar 5 ga watan Satumban 2020.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng