Dokin zuciya: Bidiyon yadda mai Keke Napep ya dambace da jami'an FRSC a Edo
Na'urar daukan hoto, ta hasko bidiyon wani direban babur mai kafa uku wanda aka fi sani da Keke Napep, yana dambacewa da wasu jami'an hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC).
Wannan lamari ya faru ne a kan babbar hanyar Benin zuwa Sapele da ke jihar Edo a Kudu maso Yammacin Najeriya.
A bidiyon da jaridar Premium Times ta wallafa, mutumin ya hau dokin zuciya, inda ya tube kayan jikinsa daga shi sai dan gajeren wando, kuma yayi kekam a kan saman motar jami'an na FRSC.
Cikin fushi da ba a san dalilinsa ba, ya sanya matukin baburin mai kafa uku ya dare kan motar ma'aikatan kuma ya ce ba zai sauka ba.
Daga karshe mutumin ya daka tsalle ya cakumo daya daga cikin jami'an yana sinka masa naushi tare da yaga masa kaya, yana cewa sai da fa a kashe shi.
Ganin wannan lamari ya sanya sauran abokan ma'aikacin suka mayar da martani na yi wa mutumin taron dangi, inda suka rika tafka masa mari da kuma lugude na naushi.
A cewar kakakin hukumar FRSC, Bisi Kazeem, ya ce wannan lamari ya auku ne da sanyin safiyar ranar Lahadi. Ya ce an kama mutumin da laifin sabawa dokar tuki.
Babban jami'in hukumar ya ce a yayin dauki ba dadin da aka yi, mutum ya keta kayan aikin wani jami'i daya, gami da fashe gilashin gaba da lallata wasu bangarori na jikin motar ma'aikatar da dutse.
KARANTA KUMA: Rashin shugabanni na gari yana ƙara rashawa a Najeriya - Sanusi II
Mista Kazeem ya bayyana martanin jami’an na FRSC a matsayin wata dabara ta kare kai da ake amfani da ita don hana shi sake kai hari kan ma’aikatan da motar su.
Mista Kazeem ya sanar da cewa, za a gurfanar da mutumin wanda tuni ya shiga hannu a gaban kotu kamar yadda doka ta yi tanadi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng