Gobe za mu saki sakamakon bincikenmu kan mutuwar Tolulope Arotile - Hukumar NAF

Gobe za mu saki sakamakon bincikenmu kan mutuwar Tolulope Arotile - Hukumar NAF

Hukumar mayakan saman Najeriya, NAF, ta bayyana cewa ranar Lahadi za ta saki bayanin binciken da ta gudanar kan abinda ya kai ga mutuwar jarumar Soja, Tolulope Arotile.

Soja mace, matukiyar jirgin yaki mai saukar angulu ta farko a tarihin Najeriya ta mutu ne ranar Litinin sakamkakon raunukan da ta samu a kai bayan bugeta da akayi da mota cikin sansanin Sojin sama dake Kaduna.

Hukumar ta ce wani tsohon abokin karatunta ne ya bigeta da mota yayinda ya juya yana mai kokarin gaisawa da ita.

Ta kara da cewa an tsare wanda ke cikin motar lokacin da aka bugeta kuma ana cigaba da gudanar da bincike, Cewar Jaridar Punch.

Diraktan yada labaran hukumar, Air Commodore Ibikunle Daramola, a jawabin da ya saki daren Lahadi yace: "Gobe, 19 ga Yuli 2020, hukumar mayakan sama zata yi hira da manema labarai domin bayani kan sakamakon binciken farko da aka gudanar kan abubuwan da suka tattari mutuwar Tolulope Arotile."

"Hakan zai gudana ne a dakin tunawa da Air Marshal MD Umar dake hedkwatar da hukumar NAF Abuja misalin karfe 2 na rana."

Gobe za mu saki sakamakon bincikenmu kan kisan Tolulope Arotile - Hukumar NAF
Gobe za mu saki sakamakon bincikenmu kan kisan Tolulope Arotile - Hukumar NAF
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yan Najeriya 70,000 daga Sokoto da Katsina sun tsere zuwa Nijar

Jiya Legit ta kawo muku cewa Hukumar mayakan saman Najeriya NAF ta bayyana cewa za'a yi jana'izar matukiyar jirgi mai saukar angulu ta farko a tarihin Najeriya, Tolulope Arotile ranar Alhamis, 23 ga Yuli, 2020.

Za'a birneta ne a makabartar hafsoshin Sojin Najeriya dake unguwar Karmajiji, birnin tarayya Abuja.

Hukumar ta bayyana hakan ne yayinda ministar harkokin mata, Pauline Tallen; ministan labarai, Lai Mohammed, da mambonin majalisar dattawa suka kai gaisuwar ta'aziyya.

A jawabin da kakakin hukumar, Ibikunle Daramola, da ya saki a shafin Tuwita, ya bayyana cewa za'a birneta cikin kwalliya na musamman da ake yiwa manyan hafsoshi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel