Sojoji sun kona gidaje da makaranta a wani garin jihar Taraba

Sojoji sun kona gidaje da makaranta a wani garin jihar Taraba

An zargi Jami'an Sojojin Najeriya na atisayen Operation Whirl Stroke da kona gidaje da makaranta a garin Peva, karamar hukumar Takum, a jihar Taraba.

Jaridar Punch ta samu hira da mazauna garin inda suka bayyana cewa mutan gari sun tsere yayinda Sojojin suka far ma garin suna kona muhallan jama'a.

Nathan Tyozaenda ya bayyana maneman labaran Punch ta wayar tarho cewa an kona makaranta mallakin Paul Gaza, da safiyar Asabar, 18 ga watan Yuli, 2020.

Tyozenda ya ce Sojojin atisayen Operation Whirl Stroke sun babbaka gidajen shugaban kasuwar doyar Peva, Mr. Orhemba, Mr. Iermber Vaatyough, da Prince Iordye Gaza.

Sojoji sun kona gidaje da makaranta a wani garin jihar Taraba
Sojoji sun kona gidaje da makaranta a wani garin jihar Taraba
Asali: UGC

KU KARANTA: Yadda Bam ya hallaka yara 6 kuma ya jikkata 5 a Malumfashi (Hotuna)

Shugaban al'ummar kabilar Tibi na karamar hukumar Takum, Hon. Peter Suleagbough, ya yi Alla-wadai da irin wadannan hare-hare da lalata dukiyan al'umma.

Ya kara da cewa kwanakin baya Sojoji sun aikata irin haka a kauyen Gberifan da Tse-Iorver.4

Yace: "Idan suna neman yan ta'adda kamar yadda suke ikirari, me zai sa su kona dukiyar mutane?"

"Menene alakar makarantar kudi, gidajen mutane da yan ta'adda."

"Kamata yayi Sojoji su rika damke yan ta'addan da suke nema ba kona dukitar mutane ba."

Amma yayinda aka tuntubi kwamandan Operation Whirl Stroke, Manjo Janar Adeyemi Yekini, ya ce ba zai ywu Sojoji haka kawai su kona gidajen mutane ba.

Yace: "Hukumar Sojin Najeriya mai hankali ce da ke aikata abubuwanta bisa rahoto mai inganci kuma ba za a kona dukiyar mutane haka kawai ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng