Yadda Bam ya hallaka yara 6 kuma ya jikkata 5 a Malumfashi (Hotuna)

Yadda Bam ya hallaka yara 6 kuma ya jikkata 5 a Malumfashi (Hotuna)

Akalla yara biyar sun rasa rayukansu yayinda shida sunyi mumunan jikkata bayan Bam ya tashi da su a kauyen 'Yar mama dake karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina.

Hukumar yan sandan jihar sun ce yara biyar suka mutu amma masu idanuwan shaida sun bayyana cewa yara 6 ne.

Wannan abu ya faru ne yau Asabar, 18 ga watan Yuli, 2020.

Bisa jawabin da kakakin hukumar, Gambo Isha, ya ski, tashin Bam din ya auku ne cikin gonan wani Malam Hussaini Mai Kwai.

Ya ce hukumar ta kaddamar da bincike cikin lamarin.

Gambo Isah ya bayyana cewa yara guda 11 na yankan ciyawa ne don ciyar da dabbobi lokacin da abin ya auku.

Yayinda biyar suka mutu kai tsaye lokacin, an garzaya da shida Asibitin garin Malumfashi domin jinya.

KU KARANTA: Menene banbanci tsakanin ciwon zazzabin sauro da cutar Korona?

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel