Menene banbanci tsakanin ciwon zazzabin sauro da cutar Korona?

Menene banbanci tsakanin ciwon zazzabin sauro da cutar Korona?

Kwanakin baya, mu'assain gidan talabijin na AIT, Raymond Alegho Dokpesi, ya kamu da cutar Korona tare akalla 'yaya da jikokinsa 8.

Bayan kwashe makkoni yana jinya a cibiyar killacewa asibitin koyarwan jami'ar Abuja, ya samu waraka ranar 15 ga Mayu, 2020 kuma aka sallamesa.

Maganarsa na farko bayan sallamarsa shine "ni fa akwai wata tambaya da nike da shi, shin menene banbanci tsakanin Malariya da Korona? dukkan magungunan da aka bamu an Malariya ne"

Wannan magana da yayi ya jawo cece-kuce tsakanin masu sharhi kan lamuran yau da kullum inda wasu suka ce mara godiyan Allah ne kuma yana kokarin batawa gwamnati suna.

Hakazalika wasu sun ce lallai jawabin Dokpesi ya jaddada musu cewa cutar Korona karya ce, kawai ciwon zazzabin sauro ne.

Amma binciken Kimiyya ya nuna cewa akwai fuskan kamanceceniya tsakanin Korona da Malariya, amma ba abu daya bane.

KU KARANTA: El-Rufa'i ya umurci ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki

Ga alamomin cutar Korona da ya kamata ka sani:

1. Tari da lamin baki ko gujewar jin kamshi ko wari

2. Tari da wahalan numfashi

3. Tari da gudawa

4. Tari da mura

5. Tari da kasalar jiki

6. Tari da rawan jiki

7. Tari da ciwon jiki

8. Tari da ciwon kai

9. Tari da ciwon makogwaro

10. Zazzabi da lamin baki ko gujewar jin kamshi ko wari

11. Zazzabi da wahalan numfashi

12. Zazzabi da gudawa

13. Zazzabi da mura

14. Zazzabi da kasalar jiki

15. Zazzabi da rawan jiki

16. Zazzabi da ciwon jiki

17. Zazzabi da ciwon kai

18. Zazzabi da ciwon makogwaro

Idan ka waye gari da daya cikin wadannan alamomi 18, ka tuntubi hukumar NCDC da wuri

Za ka iya samun lambar ofishin hukumar ta jiharka a nan https://covid19.ncdc.gov.ng/contact/

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel