Jam'iyyun Siyasa 35 sun hada kai da PDP don kifar da APC a zaben jihar Edo

Jam'iyyun Siyasa 35 sun hada kai da PDP don kifar da APC a zaben jihar Edo

- Yayinda ake shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Edo, jam'iyyu siyasa 35 sun hada karfi da jam'iyyar PDP

- Jam'iyyun sun hada kai ne domin kifar da jam'iyyar APC a watan Satumba

- Jam'iyyun siyasa wadanda yawanci INEC ta soke rijistarsa sun bayyana goyon bayansu ga gwamna Obaseki

Dambarwan Siyasan jihar Edo gabanin zaben gwamnan da zai gudana a watan Satumba ya dau sabon salo yayinda ake shirin yiwa jam'iyyar All Progressives Congress APC taron dangi.

Jam'iyyun adawan dake jihar sun hada kai da Peoples Democratic Party (PDP) domin hana mulki komawa hannun APC.

A cewar Channels TV, jam'iyyu 35 sun alanta goyon bayansu ga dan takaran PDP, Godwin Obaseki,

Jam'iyyun sun hada da Social Democratic Party (SDP), Kowa Party, All Progressives Grand Alliance (APGA), United Progressive Party (UPP) da sauran su.

Shugaban jam'iyyar SDP, Collins Oreruan, wanda yayi jawabi madadin sauran jam'iyyun ranar Juma'a 17 ga Yuli, ya ce sun yanke shawarar hada kai da PDP ne domin tabbatar da cewa Obaseki ya lashe zaben.

Oreruan ya yi kira da PDP su sanya SDP cikin kwamitocin yakin neman zaben.

Jam'iyyun Siyasa 35 sun hada kai da PDP don kifar da APC a zaben jihar Edo
Jam'iyyun Siyasa 35 sun hada kai da PDP don kifar da APC a zaben jihar Edo
Asali: UGC

KU KARANTA: Dan majalisar APC ya ce Buhari na da rauni, ko Aisha ta fi shi kuzari, an bukaceshi yayi murabus

A bangare guda, Legit ta kawo muku rahoton cewa yayinda ake shirye-shiryen zaben gwamna a jihar Edo, wanda za a gudanar a watan Satumba, wasu sun sanya wani bidiyo a katon allon majigi inda masu tafiya a kafa da mota za su iya gani.

Bidiyon yana nuna gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yana cusa daloli cikin aljihunsa.

Wani mai rajin kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju ya wallafa bidiyon a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuli.

Za ku tuna cewa a shekarar 2018 gwamnan Kanon ya fada a wata badakala na zargin aikata rashawa, bayan wani bidiyo da ya billo ya hasko shi yana zuba daloli a aljihu wanda aka ce cin hanci ne ya karba daga yan aikin kwangila.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel