Dan majalisar APC ya ce Buhari na da rauni, ko Aisha ta fi shi kuzari, an bukaceshi yayi murabus

Dan majalisar APC ya ce Buhari na da rauni, ko Aisha ta fi shi kuzari, an bukaceshi yayi murabus

Shugabannin Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) shiyar karamar hukumar Mashi, jihar Katsina, sun nuna bacin ransu kan jawaban dan majalisa mai wakiltar mazabar Mashi/Dutsi a majalisar wakilai tarraya, Mansur Mashi yayi.

Sun bukaceshi yayi murabus bisa kalaman batanci da yayi kan shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Wani jami'in jam'iyyar ya ce idan ko yaki yin murabus, sai al'ummar mazabarsa sun yi masa kiranye.

Yayin hira da manema labarai, shugaban jam'iyyar APC na Mashi, Armaya'u Doka, ya ce jawabin ya kaskantar da mambobin jam'iyyar a mazabarsa da Najeriya.

Kwafin jawabin da jaridar Premium Times ta samu ranar Juma'a, Armaya'u Doka ya yi kira ga yan majalisar dokokin tarayya su dakatad da shi bisa maganganun batancin da yayi.

KU KARANTA: Hukumar Sojin Sama ta bayyana ranar Jana'izar Tolulope Arotile (Hotuna)

Dan majalisar APC ya ce Buhari na da rauni, ko Aisha ta fi shi kuzari, an bukaceshi yayi murabus
Dan majalisar APC ya ce Buhari na da rauni, ko Aisha ta fi shi kuzari, an bukaceshi yayi murabus
Asali: UGC

Yace: "Dan majalisar ya ce Buhari ya kau kamar yadda marigayi Yar'adua yayi, saboda Yemi Osinbajo ya dau ragamar mulki, hakan kawai kasar nan za ta cigaba daga yanzu zuwa 2023."

"Muna kira da APC a jihar da kasa ta ladabtar da shi kuma majalisa ta dakatad da shi kan maganganun da yayi."

"Idan ko ba'a yi haka ba, a matsayinmu na mambobin mazabarsa na da hakkin daukan mataki kansa."

Wani jigon jam'iyyar APC a karamar hukumar Mashi mai suna Hanarabul ID ya bayyanawa Premium Times cewa, "Rikodin dinsa da akayi ya tona masa asiri. Dukkanmu mun saurara."

A faifan rikodin din, dan majalisar tare da wasu dake hira da shi ya bayyana cewa uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta fi shugaban kasa kuzari.

An ji yana cewa: "Bari in fada muku, da Aisha da karfin da Turai Yar'adua ta samu lokacin Yar'adua, da Najeriya ta fi cigaba fiye da yadda take yanzu karkashin Buhari. Ta fi shi kuzari da wayau."

"Kuma ko lokacin da marigayi shugaban fadar Buhari (Abba Kyari) ya rasu, na fadawa mutane cewa za su ga ainihin raunin Buhari cewa ba Kyari bane matsalan, Buhari ne. Ku kalla yanzu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel