Babu sauran mai Korona a jihar Sokoto, Zamfara da Kogi

Babu sauran mai Korona a jihar Sokoto, Zamfara da Kogi

Alkaluma daga hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC sun nuna cewa jihohi uku a Najeriya sun waye gari babu sauran masu cutar Korona cikinsu.

Wadannan jihohin sun hada da Sokoto, Zamfara da Kogi.

A jihar Zamfara, mutane 76 ne suka kamu da cutar tun lokacin da ta bulla, yayinda 71 suka samu waraka kuma aka sallamesu, mutane 5 sun mutu sakamakon haka.

Sama da makonni hudu kenan ba'a samu sabon mai cutar ba. Jihar Zamfara ce jiha daya da ta dade ba'a kara samun mai cutar ba.

A bangaren jihar Sokoto, mutane 153 ne suka kamu da cutar tun lokacin da ta bulla, yayinda 137 suka samu waraka kuma aka sallamesu, mutane 16 sun mutu sakamakon haka.

A jihar Kogi kuwa, mutane 5 ne suka kamu da cutar tun lokacin da ta bulla, yayinda 3 suka samu waraka kuma aka sallamesu, mutane 2 sun mutu sakamakon haka.

Hukumar NCDC na kuka da rashin bada hadin kai ta bangaren gwamnatin jihar Kogi.

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 595 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:53 na daren ranar Alhamis 16 ga Yulin shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 595 da suka fito daga jihohin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel