Yan Najeriya 70,000 daga Sokoto da Katsina sun tsere zuwa Nijar
Sama da yan Najeriya 70,000 sun tsere daga kasar zuwa Jamhurriyar Nijar sakamakon hare-haren yan bindiga da ya addabi al'ummar arewa maso yammacin kasar, HumAngle ta laburto
Bayan rashin rayuka, dukiya da muhallansu, yan gudun hijra a jihohin Zamfara, Katsina da Sokoto sun yi alhinin yadda gwamnatin Najeriya tayi watsi da su.
A cewar hukumar kula da yan gudun hijra na majalisar dinkin duniya (UNHCR), a watan Afrilu 2020, akalla yan Najeriya 23,000 ne suka arce zuwa kasar Nijar domin kare rayukansu saboda yan bindiga sun ragargajesu.
Daya daga cikin matasan da suka gudu, Nasuru Lawal, ya bayyanawa manema labaran HumAngle cewa Sojojin Najeriya sun yi watsi da su yayinda na Nijar ke kawo musu dauki.
"Tun lokacin da rikicin nan ya fara, bamu ga jami'in Najeriya ko daya ba. Sojojin Nijar ne ke kawo mana dauki. Muna da kyakkayawan alaka da su."
"Sojojin Jamhurriyar Nijar sun taimaka mana a garuruwanmu saboda ana kiransu, da wuri suke kawo mana taimako yayinda namu Sojin na Najeriya sai sun kwashe sa'o'i kafin su karaso." Yace
Wani mazaunin Mallam Magaji, wanda dan gudun Hijra ne ya bayyanawa manema labaran HumAngle cewa, "Yan bindigan da ke yankinmu na tsoron Sojojin Nijar."
"Dalilin haka shine sun san Sojojin Nijar zasu ragargajesu idan suka kawo hari, amma na Najeriya sunyi kasa a gwiwa."

Asali: Twitter
KU KARANTA: Babu sauran mai Korona a jihar Sokoto, Zamfara da Kogi
Yan gudun Hijran sun ce suna jin dadin rayuwa da al'ummar kasar Nijar kuma sun tarbesu cikin mutunci.
Wani dan gudun Hijra, Hamisu, a Garin Kaka yace "muna farin cikin alakarmu da mutanen Nijar, suna da mutunci."
"Suna taimaka mana da abinci, kaya, sun bamu bashin kudi, kuma har mun fara auratayya tsakaninmu."
HumAngle ta samu labarin cewa wasu gwamnonin Najeriya kan kai ziyara kasar Nijar amma basu taba ziyartar yan Najeriya dake sansanin gudun Hijran ba.
Wani dan gudun Hijra, Lawalli, yace "Wasu daga cikin gwamnonin Arewa maso yamma sukan zo Maradi domin kallon wasannin damben da ake shiryawa a Garin Kaka da muke zaune."
"Gwamnan jihar Sokoto na cikinsu amma sai ya sharemu ya koma gida."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng