Yadda na dinga karuwanci da juna biyu sannan da sanin mijina - Matar aure

Yadda na dinga karuwanci da juna biyu sannan da sanin mijina - Matar aure

Tubabbiyar karuwa, Purity Wanjiru mai shekaru 25 a garin Nairobi a kasar Kenya ta bayyana abubuwan da ta fuskanta yayin da take titi.

Ta ce a wani lokaci da ya gabata tayi aure kuma ta zauna tare da mijinta wanda ta kwatanta da miji mara kula. Ta ce ya san tana karuwanci amma bai taba hana ta ba ko kuma ya nuna damuwarsa.

Hatta lokacin da take da ciki, ta ci gaba da karuwancinta a titi. Mijinta bai damu da hakan ba don bai ce komai a kai ba.

Wanjiru, wacce aka haifa a Uthiru da ke yankin Kiambu, ta tuna yadda ta koma titi bayan da ta samu rashin jituwa tsakaninta da iyayenta.

Ta kwatanta yarintarta da wacce ke cike da tawaye ga iyayenta, wanda hakan yasa basu jituwa. Hakazalika, karatunta kwata-kwata bai yi zurfi ba.

Ta tuna yadda bata iya wuni daya a makaranta domin tana jin bukatar fita yawo a titi. Tun tana makarantar firamare, tana barin aji ta tafi yawo.

A yayin da take aji biyar, an dakatar da ita a makaranta tare da umarnin cewa sai ta sauya halayyarta za a amince da ita.

"A gidanmu mu 12 ne. Akwai wani lokaci da yayyina suka taru suka min duka saboda ni ce auta kuma ina nuna halin rashin son karatu. Ina da shekaru 13 na gudu na bar gida," tace.

Wannan hukuncin ne ta fara rayuwar titinta. Ta tuna yadda ake kama ta saboda yawon da take a titi tare da karuwanci tun tana karama.

Ta ce bayan fitowarta daga gidan yari, wata mata ta dauketa inda take mata ayyukan gida. Wanjiru ta amince.

Yadda na dinga karuwanci da juna biyu sannan da sanin mijina - Matar aure
Yadda na dinga karuwanci da juna biyu sannan da sanin mijina - Matar aure. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa

Amma kuma bayan kwashe watanni tare da matar, ta yanke hukuncin komawa titi saboda yawan aikin da take lafta mata.

A yayin da take kan titin kuma da yarintarta, ta hadu da wani matashi da yace zai aureta. Daga nan ta koma gidansa. Bayan aurensu da watanni kadan ta samu juna biyu amma babu dadewa ya fara dukanta.

"Dan giya ne kuma dan kwaya. Kudinsa a can suke karewa. Saboda haka ya daina kula da ni," Wanjiru tace.

"A haka yake zagina tare da cin zarafi daban-daban."

Wanjiru ta ce zagin da yake mata yana damunta ba kadan ba. Daga nan makwabtanta suka nuna mata hanyar samun kudi don ciyar da kanta da jinjirin da ke cikinta.

Ta ce daga nan ta shirya bai wa duk namijin da yake so jikinta amma in har zai bada kudi, duk da cikin da ke jikinta.

Bayan tsufan cikinta, ta haifa yarinya mace. Bayan watanni kadan, ta koma titi saboda mijinta bai damu da ita ba tare da jaririyarta.

"Ya ce zai iya bamu abinci ne a lokacin da ya kamata amma sauran bukatun jaririyar, sai dai in dauka nauyi," tace.

"Abu mafi bada mamaki shine yadda nake barin mishi diyata don ya kula da ita da dare yayin da nake fita karuwancina," tace.

"Idan na dawo da safe, ya kan tambayeni ya aiki kuma nawa na samu. Duk da ina samun kudi, ina jin kunyar aikin da nake yi. Na san kazamin aiki ne kuma bani da daraja," ta kara da cewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel