Yanzu-yanzu: Rashin jituwa a majalisar dokokin jihar Neja, an tsige shugaban masu rinjaye da mataimakinsa

Yanzu-yanzu: Rashin jituwa a majalisar dokokin jihar Neja, an tsige shugaban masu rinjaye da mataimakinsa

Mambobin majalisar dokokin jihar Neja sun tsige shugaban masu rinjayen majalisar, Hanarabul Suleiman Nasko, da mataimakinsa Hanarabul Andrew Jagaba.

Hakan ya biyo bayan kudirin da dan majalisa, Ndagi Baba, mai wakiltar mazabar Lavun ya shigar kuma Saidu Tama, mai wakiltar Edati ya goyi bayansa a zaman ranar Alhamis.

Yayinda yake magana kan lamarin, Ndagi Baba ya ce sun lura cewa shugaban masu rinjayen da mataimakinsa ke hana ruwa gudu a gidan kuma majalisa ba ta samun cigaba karkashinsu.

Punch ta ruwaito cewa kakakin majalisar, Abdullahi Wuse, ya ce bada saninsa aka shirya tsigesu ba kuma hakan ya sabawa dokokin majalisar.

Mohammed Haruna, mai wakiltar mazabar Bida II, ya ce kawai a tsigesu kuma Malik Madaki mai wakiltar mazabar Bosso, ya mara masa baya.

Bayan tsigesu, Yabagi Akote, mai wakiltan mazabar Gbako ya bada shawaran maye gurbin da Abba Bala.

Hakazalika aka nada Binta Mamman, mai wakiltar mazabar Gurara, a matsayin sabuwar mataimakiyar shugaban masu rinjaye.

Yanzu-yanzu: Rashin jituwa a majalisar dokokin jihar Neja, an tsige shugaban masu rinjaye da mataimakinsa
majalisa
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel