Yanzu: Shugaba Buhari ya kaddamar da cinikayyar gwal, mutane 250,000 zasu samu aiki

Yanzu: Shugaba Buhari ya kaddamar da cinikayyar gwal, mutane 250,000 zasu samu aiki

- Shugaban kasa Muhammadu Buhasri ya kaddamar da shirin PAGMDI da nufin samawa sama da mutane 250,000 aiki ga 'yan Nigeria

- Wannan shirin zai taimaka wajen kawo karshen hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a kasar da kuma samawa gwamnatin tarayya $500m a duk shekara

- A wani bangaren kuma, babban bankin Nigeria, CBN ya biya N268m domin sayen gwal na farko da Nigeria ta hako ta kuma sarrafa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, ya jagoranci wani taro na yanar gizo inda ya kaddamar da shirin fadar shugaban kasa na bunkasa hakar gwal (PAGMDI).

Rahotanni sun bayyana cewa, shirin PAGMDI, zai samawa 'yan Nigeria akalla 250,000 ayyuka, yayin da gwamnatin tarayya zata rinka samun kudaden shiga $500m a kowacce shekara.

A cewar wata sanarwa daga Femi Adesina, mai tallafawa shugaban kasa ta fuskar watsa labarai, shirin zai taimaka wajen kawo karshen hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba da kuma baiwa Nigeria kwarin guiwar samun makoma mai kyau a nan gaba.

"Wannan babban shirin zai tallafa wajen samar da ayyukan yi ga 'yan Nigeria, samar da kudaden shiga, da kuma bunkasa kudaden ajiyar waje na gwamnati.

"A yanzu da aka kaddamar da shirin PAGDMI wanda zai kai ga bude cibiyoyin sayar da gwal a wasu muhimman garuruwa, masu hakar ma'adanai da kananan 'yan kasuwa da ke cinikayyar gwal zasu samu damar barje guminsu.

KARANTA WANNAN: Muna da tabbaci: PDP zata samu nasara kan APC a zaben Ondo - Ekweremadu

"Ire iren wadannan ayyukan zasu taimaka wajen bunkasa kudaden shigar kasarmu. Cinikayyar gwal a cibiyoyin da aka amince da su zai taimakawa gwamnati wajen samu kudade da alfarmu daga sayar da hajojoji na gwal.

"Wannan shirin zai taimaka wajen bunkasa kudaden ajiyar waje na gwamnati ta hanyar baiwa babban bankin Nigeria damar kara yawan adadin gwala gwalan da ke ajiye a lalitarta."

A wani labarin kuma, babban bankin Nigeria CBN ya biya zunzurutun kudi har N268.6m domin sayen gwal mai nauyin 12.5kg, gwal din da Nigeria ta fara haka da kanta kuma ta sarrafa shi bisa ka'idar nagartar LBMA. A yanzu gwal din ya zama cikin kadarorin Nigeria da ta ajiye.

Ga hotunan taron a kasa:

Yanzu: Shugaba Buhari ya kaddamar da cinikayyar gwal, mutane 250,000 zasu samu aiki
Yanzu: Shugaba Buhari ya kaddamar da cinikayyar gwal, mutane 250,000 zasu samu aiki Source: Twitter
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel