Muna da tabbaci: PDP zata samu nasara kan APC a zaben Ondo - Ekweremadu

Muna da tabbaci: PDP zata samu nasara kan APC a zaben Ondo - Ekweremadu

- Sanata Ike Ekweremadu ya bayyana dalilin da ya sa PDP zata samu nasara kan APC a zaben gwamnan jihar Ondo da za a gudanar a watan October

- Ekeremadu ya yi jawabi a Akure a lokacin da yake sa ido kan zaben wakilan jam'iyyar da suka fito daga kananan hukumomi 18 na jihar

- Ya ce yana da tabbaci jam'iyyar PDP zata sake darewa kujerar gwamnan jihar kasancewar suke da sanatoci biyu cikin uku da jihar take da su

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijai Ike Ekweremadu ya bayyana dalilin da ya sa jam'iyyar PDP zata samu nasara kan jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Ondo za a gudanar a cikin watan October.

Wakilin mazabar Enugu ta Yamma ya ce a halin yanzu jam'iyyar PDP ta warware dukkanin matsalolinta na cikin gida musamman zanga zangar da aka alakantata da shi da ya tilasta kafa kwamitin zabe na mutane uku.

Ekeremadu ya yi jawabi a Akure a lokacin da yake sa ido kan zaben wakilan jam'iyyar a matakin kasa da kuma wani mai nakasa guda daya daga kananan hukumomi 18 na jihar.

Wakilan zaben da nakasassun zasu yin hadaka da kwamitin mutane uku domin gudanar da zaben fidda gwani na jam'yyar PDP a ranar Laraba mai zuwa.

Ekweremadu ya tabbatar da cewa za a gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP reshen jihar Ondo a ranar da aka tsara, domin kuwa tuni aka warware matsalar wakilan zaben.

A cewarsa: "Batu kan wani kwamitin wakilan zabe na mutum uku da akayi an warware shi. Akwai wasu korafe korafe da aka gabatar kuma naji dadin yadda aka magance matsalar. Zaben fidda gwani na jihar Ondo na jami'iyyar PDP zai gudanar kamar yadda aka sanya a ranar 22 ga watan Yuli.

KARANTA WANNAN: MAKIA: Ban ci zarafin ma'aikacin tashar jirgin sama ba - Abdul'aziz Yari

"Zaku iya bayar da tabbaci kan yadda aka gudanar da zaben wakilan zaben ba tare da matsala ba. Munji dadin ganin sakamakon. Babu tashin hankali. Ba a samu wani da karya dokar zabe ba.

Muna da tabbaci: PDP zata samu nasara kan APC a zaben Ondo - Ekweremadu
Muna da tabbaci: PDP zata samu nasara kan APC a zaben Ondo - Ekweremadu Source: Twitter
Asali: Depositphotos

"A halin yanzu, jam'iyyar PDP ta mayar da hankali wajen ganin ta koma kan mulki a jihar. Naji dadi ganin yadda kowa ya mayar da hankali wajen ci gaban jihar. Mun samu babbar nasara duk da cewa mun rasa mulki na shekaru hudu. A yanzu zaku iya gani da idanuwanku.

"A babban zaben da ya gabata na kasa, muna da sanatoci biyu ne a cikin uku, hakan na nufin muna da kaso biyu saman uku a manyan mukaman jihar. Wannan na kuma nufin jam'iyyar zata yi nasarar samun kujerar gwaman jihar."

A wani labarin kuma; Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari, ya karyata rahotannin da ke yawo na cewar ya ci zarafin wani ma'aikacin tashar jiragen sama a ranar Asabar, a tashar sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano (MAKIA), Kano.

Haka zalika, Yari ya bayyana cewar ya zama wajibi hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta kasa FAAN, ta janye maganganun da tayi a shafinta na Twitter kan cewar ya karya ka'idoji, da kuma rubuta wasikar ban hakuri akan sharrin da tayi masa.

Yari a cikin wata sanarwa daga mai bashi shawara kan kafofin watsa labarai, Mayowa Oluwabiyi, ya ce duk da cewa yayi amfani da tashar jirgin a wannan rana, amma abunda ake zarginsa da shi bai aikata ba. Idan za a iya tunawa a ranar Laraba hukumar FAAN a shafinta na Twitter ta wallafa cewa bijirewa matakan kariya na COVID-19 da Yari ya yi abun Allah wadai ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel