Yanzu-yanzu: Gwamna Wike ya kwaci matar da ta zargi Akpabio da neman jima'i da ita bayan yan sanda sun yiwa gidanta zobe

Yanzu-yanzu: Gwamna Wike ya kwaci matar da ta zargi Akpabio da neman jima'i da ita bayan yan sanda sun yiwa gidanta zobe

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya kwace tsohuwar MD na hukumar cigaban yankin Neja Delta NNDC, Joi Nunieh, bayan an garkameta cikin gidanta dake Port Harcourt, babbar birnin jihar.

Bidiyon TVCNews ya nuna yadda gwamnan ya shiga cikin gidan kuma ya umurci yan sandan su fice sannan ya tafi da ita.

Mun kawo muku rahoton cewa Jami'an 'yan sandan Najeriya sun tsinkayi gidan Joy Nunieh, tsohuwar mukaddashin manajan daraktan hukumar habaka yankin Neja Delta (NDDC), inda suka yi masa zobe.

Jami'an tsaron sun isa gidan ne da ke lamba 3, titin Owuru Creek, kusa da titin Herbert Macauley da ke tsohuwar GRA a Fatakwal, jihar Ribas a sa'o;in farko na ranar Alhamis.

Wannan ya faru ne kafin isar Nunieh gaban kwamitin bincike na majalisar dattawa da ke Abuja inda za ta amsa tambayoyi a kan ayyukan NDDC.

A yayin da jaridar The Cable ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ribas, Omoni Nnamdi don tsokaci, ya bukaci a kira sa nan da mintuna 30.

Nunieh, a wata tattaunawa da aka yi da ita a baya bayan nan, ta zargi ministan da cin hanci da rashawa, cin zarafi da kuma muzgunawa ma'aikata, fasa bututun mai, shiga cikin ayyuka kungiyoyin asiri, karya dokokin aikinsa da sauransu.

Hakazalika ta zargeshi da kokarin taba mata jiki da kwaciya da ita amma ta waska masa mari a cikin gidansa dake unguwar Apo dake birnin tarayya Abuja.

Amma Ministan na gaban yankin Niger Delta, Godswill Akpabio, ya karyata zarginsa da Ms. Gbene Joi Nuneih, na cewar ya yi kokarin zina da ita.

Ministan, a cikin wata sanarwa da ya bayar a ranar Laraba a Abuja ta hannun Aietie Ekong, hadiminsa ta fuskar watsa labarai, ya ce wannan zargin da ta yi wasa, "karyace kawai tsagoronta".

"Duk kalamanta karairayi ne kawai, babu gaskiya a ciki.

"Ministan bai aikata ba, ko a wani waje, ko a wani lokaci, ko a cikin wani hali, bai ci zarafin Ms. Nunieh, balle ma har ace ya yi yunkurin kamanta wani abu da ya shafi fyade ga Ms. Nunieh, ko kuma wata mace a cikin ma'aikatar ko hukumar NDDC," a cewar sanarwar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel