Fulanin Daddo Pulaku sun bukaci kashi 4% na filaye a Bauchi domin dakile rikicin makiyaya da manoma

Fulanin Daddo Pulaku sun bukaci kashi 4% na filaye a Bauchi domin dakile rikicin makiyaya da manoma

Wata gamayyar hadin gwiwa ta kungiyoyin Fulani mai suna Daddo Pulaku a jihar Bauchi, ta shigar da bukata da kuma sharadin kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a jihar.

Kungiyar ta shigar da bukatar neman a bai wa makiyaya kashi 4 cikin 100 na fadin kasar Bauchi domin ci gaba da dabdala da dabbobinsu na kiwo.

Bukatar tana kunshe ne a cikin wata takardar sanarwar da kungiyar ta gabatar ga Kwamitin Gudanar da Bincike ka Rikicin Kasa a ranar Laraba yayin da daidaikun mutane da kungiyoyi ke ci gaba da gabatar da wasika a gaban kwamitin.

Kungiyar Daddo Pulaku ta jaddada cewa, ya kamata gwamnati ta tabbatar da aiwatar da cikakkiyar dokar samar da filayen kiwo kamar yadda yake kunshe a cikin kudirin da aka zartar a shekarar 2018.

Makiyaya
Hoto daga jaridar Guardian
Makiyaya Hoto daga jaridar Guardian
Asali: Depositphotos

Ta yi tuni kan kudirin da ya haramta noma gonaki a gabar kowace babbar hanyar tare da bayar da tazara ta tsawon mita 30 daga magudanar ruwa da ke gabar titunan har zuwa gonaki.

Muhammad Aminu Tukur, Shugaban kungiyar Daddo Pulaku ta jihar Bauchi, shi ne ya rattaba hannu a kan takardun shigar da bukatar a madadin sauran shugabannin kungiyar.

Sanarwar ta bayyana cewa, "ba wai kawai a jihar Bauchi ba, makiyaya a Najeriya da kuma yankin Afrika ta Yamma na fuskantar barazanar wannan mummuna tashin hankali da ke ci gaba da yawaita a duk shekara idan ma ba kullum ba."

"Abin takaici shi ne yadda masu ƙalubalantar 'yancinmu na rayuwa da zaɓin da muka yi a kan wannan sana'a ta kiwo, sun fi kowa kwadayi da zalama ta son cin nama da shan madarar shanu."

KARANTA KUMA: Gwamna Ganduje ya sauya fasalin majalisar zartarwa ta Kano

Kamar yadda jaridar Daily Sun ta ruwaito, makiyaya su na fuskantar mummunar barazana a duk kananan hukomi 20 na jihar Bauchi, inda lamarin yafi kamari a Itas/Gadau, Ganjuwa da karamar hukumar cikin birni.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa, masu unguwanni, dagatai da kuma ma'aikatan kula da kasa, na ci gaba da rarraba filayen kiwo a tsakaninsu.

Kungiyar Daddo Pulaku ta yi kira ga kwamitin da ya zabi hanyar shanu guda daya a ko ina cikin jihar da kuma ziyarta domin tabbatar da abin da take fada.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel