Yanzu-yanzu: Dakarun Sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram a Borno (Hotuna)
Dakarun mayakan saman Najeriya sun ragargaji yan ta'addan Boko Haram a sansaninsu inda suka hallaka dimbin mayakan a ruwan wutan da sukayi a Ngwuri Gana a jihar Borno.
Hedkwatar tsaro ta bayyana hakan a jawabin da ta daura a shafinta na Tuwita ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, 2020.
Hukumar ta bayyana cewa Dakarun sun kai hari ne jiya Laraba a yankin Gulumba Gana zuwa Kumshe dake Arewacin jihar Borno.
Jawabin yace: "Yayinda ake cigaba da kai farmaki kan yan ta'adda a yankin Arewa maso gabashin kasar nan, mayakan saman rundunar Operation LAFIYA DOLE a jiya, 15 ga Yuli,2020 ta ragargaza sansanin yan Boko Haram kuma sun kashe dimbinsu a Ngwuri Gana dake hanyar Gulumba Gana zuwa Kumshe dake Arewacin jihar Borno."
"An kai farmakin ne sakamakon rahoton leken asirin da ya nuna cewa yan ta'addan na amfani da sansanin wajen shirya yadda za'a kaiwa Sojoji hari a yankin Kumshe."
"Hakazalika jiragen leken asiri sun tabbatar da kasancewan dimbin yan ta'addan Boko Haram a wajen, inda aka ga wasu rike da makamansu."
"Daga baya akayi amfani da jiragen yaki da masu saukar angulu wajen kai hari wajen."
"A harin, an ragargaji gidajen dake wajen tare da kashe dimbin yan ta'addan."

Asali: UGC
KU KARANTA: Ya kamata a fara dandake masu fyade - Kakakin Majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila
Kalli hotunan:
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng