Muna kan bakanmu, ba za a yi jarabawar WAEC bana ba - Gwamnatin tarayya

Muna kan bakanmu, ba za a yi jarabawar WAEC bana ba - Gwamnatin tarayya

Yayinda yan Najeriya ke cigaba da sukar dakatad da jarabawar WAEC da komawa makarantar daliban ajin karshe a sakandare, gwamnatin tarayya ta ce tana kan bakanta na hana daliban kasar nan musharaka bana.

Zaku tuna cewa a makon da ya gabata, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana cewa Najeriya ba zatayi musharaka a jarabawar WAEC ba saboda gudun yaduwar cutar Coronavirus.

Kungiyar masu makarantun kudi sun bayyana rashin amincewarsu da wannan kudiri kuma sun yi kira da gwamnati ta sake duba lamarin.

Hakazalika masu sharhi kan al'amuran yau da kullum, yan siyasa, da masana sun bayyana cewa rashin rubuta jarrabawar zai yi mumunan tasiri kan daliban Najeriya matuka.

Amma a ranar Laraba, gwamnatin tarayya ta jaddada matsayarta a zaman da tayi da masu ruwa da tsaki kan lamarin.

Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajuiba, ya bayyana cewa har yanzu suna tattaunawa da iyayen yara kan shawarar da ma'aikatar ilimin ta yanke.

Bayan zaman majalisar zartarwa na ranar Laraba, Nwajuiba yace "Har yanzu muna tattaunawa da iyayen yara kan matsayar ma'aikatar."

"Abinda Minista (Adamu Adamu) ya fada ne matsayar ma'aikatar; ba mu tunanin abubuwa sun daidaita yanzu. Alkaluman NCDc na da ban tsoro kuma bayyanawa iyaye da masu ruwa da tsaki."

Muna kan bakanmu, ba za a yi jarabawar WAEC bana ba - Gwamnatin tarayya
Muna kan bakanmu, ba za a yi jarabawar WAEC bana ba - Gwamnatin tarayya
Asali: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Alla-wadai da dabi'ar gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri - Hukumar FAAN

A bangare guda, Jihohin Kudu maso yamma da akafi sani da yankin kabilar Yoruba 6 sun yanke shawarar bude makarantunsu domin daliban ajin karshen a makarantun sakandare su rubuta jarabawar WAEC wata mai zuwa.

Jihohin sun hada da Lagos, Ogun, Oyo, Ondo, Osun da Ekiti.

Kwamishanonin Ilimi, masu baiwa gwamnoni shawara kan ilimi da shugabannin hukumomin ilimin jihohin sun yanke shawarar hakan ne a ganawar da sukayi ta yanar gizo.

Sun yi ittifaki lallai a bude makarantu a jihohin su bude saboda daliban ajin sakandaren karshe su zana jarabawa.

A jawabin da suka saki bayan ganawar, sun bayyana cewa dalibai su koma makaranta ranar 3 ga watan Agusta, 2020.

Wannan ya sha ban-ban da matsayar da jihohin Arewacin Najeriya suka yanke.

Kwamishanonin ilimi na jihohi 19 dake Arewacin Najeriya sun bayyana amincewarsu da dakatad da shirin bude makarantu ga daliban azuzuwan karshe da gwamnatin tarayya tayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel