Yanzu-yanzu: Alla-wadai da dabi'ar gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri - Hukumar FAAN

Yanzu-yanzu: Alla-wadai da dabi'ar gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri - Hukumar FAAN

Hukumar kula da tashoshin jirgin sama ta yi Alla-wadai da gwamnan jihar Adamawa, Alh. Ahmadu Fintiri, bisa abinda yayi ya saba ka'ida a tashar jirgin Fatakwal dake jihar Rivers.

Bayan saba doka, Hukumar ta ce wadanda ke tare da Fintiri guda 8 sun bi sahunsa.

Ya aikata hakan ne ranar Talata, 14 ga watan yuli, 2020.

A takardar da hukumar ta saki a shafinta na Tuwita, ta ce Ahmadu Fintiri ya ki amincewa a tsaftace hannusa, jakunanansa da kuma duba zafin jikinsa.

Bayan haka, direbobin da suka zo tarbansa sun shigar da motocinsu har wajen da ake ajiye jirgi kuma hakan ya sabawa dokokin tashoshin jirgin sama.

Jawabin yace: "Hukumar kula da jiragen sama a Najeriya (FAAN) ta yi Alla-wadai da dabi'ar gwamnan jihar Adamawa, Alh Ahmadu Fintiri, wanda ya dira tashar jirgin saman Port Harcourt a jirgi mai lamba 5N-IZY, misalin karfe 17:08 na ranar 14 ga Yuli, 2020."

"Shi tare da wasu mutane 8, sun take dokokin tsaro da kiwon lafiya kamar yadda gwamnatin tarayya tayi umurnin da kwamitin fadar shugaban kasa wajen yaki da COVID19 PTF ta hanyar kin amincewa a duba zafin jikinsu da tsaftacesu."

"Hakazalika dukkan wadanda suke tare da shi su takwas sun bi sahunsa."

"Bayan haka wadanda suka zo tarbansa suka shiga da motocinsu har cikin titin jirgi suna masu saba umurnin tsaro."

"Wannan irin rashin da'an na iya sanya rayukan fasinjoji cikin hadari kuma ba zamu amince da hakan ba."

"Saboda haka FAAN tana kira ga fasinjoji, musamman masu alfarma, su taimaka su bi umurnin fadar shugaban kasa wajen bin dokokin da aka gindaya domin kare rayukan kowa daga cutar Coronavirus."

Yanzu-yanzu: Alla-wadai da dabi'ar gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri - Hukumar FAAN
Adamawa, Ahmadu Fintiri
Asali: Facebook

A jiya Legit ta kawo muku rahoton cewa Hukumar kula da tashoshin jirgin sama ta yi Alla-wadai da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alh. Abdulaziz Yari, bisa abinda yayi ya saba ka'ida a tashar jirgin Malam Aminu Kano.

Bayan saba doka, Hukumar ta ce Yari ya ci mutuncin ma'aikacin muhalli ta hanyar bangajeshi.

Ya aikata hakan ne ranar asabar, 11 ga watan yuli, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: `https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel