Babu Ribaa, babu ruwa: Gwamna Zulum ya kaddamar da shirin rabawa kananan yan kasuwa bashin N1bn

Babu Ribaa, babu ruwa: Gwamna Zulum ya kaddamar da shirin rabawa kananan yan kasuwa bashin N1bn

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Laraba ya kaddamar da shirin bayar da bashin N1bn ga kanana da matsakaitan yan kasuwa a jihar, The Nation ta ruwaito.

Wakilin The Nation da ya halarci taron kaddamar da shirin ya ruwaito cewa yawancin wadanda suka ci gajiyar bashin mata ne da gamayyar kungiyoyin yan kasuwa DA suka tsaya musu jingina.

A cewar gwamnan, wannan shine shafin farko na rabon bashin milyan biyu ga kanana da matsakaitan yan kasuwa da gwamnatin jihar tare da hadin kan bankin masana'antu ke shirin yi ta hannun bankin Borno Renaissance Micro Finance Bank .

Zulum ya sanar da cewa wadanda zasu ci gajiyar wannan bashi sune kananan yan kasuwan da rikicin Boko Haram da annobar COVID-19 ta nakasa.

Ya ce wannan shirin zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin jihar, samar da ayyukan yi, tare da fadada hanyoyin samun kudi ga matasa a jihar.

Yace: "A yau, mutane 15,861, yan kungiyoyin yan kasuwa 12 zasu amfana da lamunin N994,930,000.00."

"Bashin bai bukatar kudin ruwa kuma mutum zai iya biya cikin shekaru 4 tare da damar jinkirin watanni 6 da ake kyautata zaton cewa abubuwa zasu gyaru kuma a samu riba,"

Babu Ribaa, babu ruwa: Gwamna Zulum ya kaddamar da shirin rabawa masu kananan karfi bashin N1bn
Gwamna Zulum
Asali: UGC

Ya yi kira da wadanda suka amfana da bashin nan su sanya kudin cikin kasuwancinsu kuma kada suyi watanda.

Hakazalika ya yi kira kungiyoyin su lura da mabobinsu kuma su tabbatar da cewa an biya bashin.

Ya kara da cewa: "Duk wanda ya samu nasarar biyan bashin cikin lokacin da aka kayyade, za'a yafe masa rabin kudin kuma zai cancanci kara amsan wani bashin."

Bugu da kari, gwamnan ya sanar da cewa gwamnatinsa na cikin tattaunawa da babbar bankin tarayya CBN, bankin cigaban Afrika AfDB da bankin cigaban Musulinci IDB domin samar da wasu hanyoyin amfanar kanana da matsakaitan manoma a jihar.

KU KARANTA: Hukumar kula da tashoshin jirgin sama ta yi Alla-wadai da tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel