Yanzu-yanzu: Magatakardan majalisar dattawa ya yi watsi da sallamarsa da aka yi

Yanzu-yanzu: Magatakardan majalisar dattawa ya yi watsi da sallamarsa da aka yi

Sani Omolori, magatakardan majalisar dattawa, ya ce ci gaban zamansa a ofishinsa na bisa ga shari'a ne kuma hukumar kula da ayyuka ta majalisar bata isa ta soke wannan dokar ba.

A wata takarda da jaridar The Cable ta gani a ranar Laraba,Omolori ya ce hukumar bata da karfin ikon ture wannan sabuwar dokar da majalisar dattawa da ta gabata ta tabbatar.

Ya umarci dukkan ma'aikatan da hukumar ta sallama da su yi watsi da wannan umarnin sannan su ci gaba da ayyukansu.

Yanzu-yanzu: Magatakardan majalisar dattawa ya yi watsi da sallamarsa da aka yi
Yanzu-yanzu: Magatakardan majalisar dattawa ya yi watsi da sallamarsa da aka yi. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Magatakardan majalisar tarayya da wasu ma'aikata 150 sun yi murabus

Hukumar kula da ayyukan majalisar tarayya ta kasar nan, ta amince da ritayar magatakardanta, Mohammed Sani-Omolori tare da wasu ma'aikatanta 150.

Shugaban hukumar kula da ayyukan majalisar, Ahmed Amshi, ya bada wannan sanarwar a wata takardar da jaridar The Punch ta gani a ranar Laraba.

Tun a watan Fabrairun 2020 ya kamata Sani-Omolori ya yi murabus, amma gyaran da majalisar dattawan karo ta 8 ta yi wa sharuddan aiki ne yasa aka kai shi har tsawon shekaru biyar.

Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan, ta bayyana hakan da rashin bin ka'ida tare da take doka.

A wani labari na daban, alakar da ke tsakanin ma'aikatar kwadago da majalisar dattawan kasar nan ta sake tabarbarewa a ranar Laraba a yayin da wasu wakilan majalisar da ministan kwadago, Chris Ngige suka samu rashin jituwa.

Rikicin ya fara ne bayan babban darakta a ma'aikatar kwadagon, Eyewumi Neburagho, wanda ya wakilci ministan aka gayyacesa don yin tsokaci a kan wata doka.

Kalamansa sun tada kura bayan da ya bukaci a dakatar da jin ta bakin jama'a tare da dokar har zuwa lokacin da kwamitin majalisar za su gayyaci ma'aikatar tare da tura mata dokar a rubuce.

Neburagho ya musanta cewa, a matsayinsa na daya daga cikin masu ruwa da tsaki, ba a tafiya da ma'aikatarsu a duk lokacin da aka zo jin ta bakin jama'a. Sai dai su turo wakili a duk lokacin da suka samu rahoto daga manema labarai.

Ya ce dole ne ma'aikatar ta san yadda dokar take da kuma yadda za ta shafi ma'aikatanta.

A don haka, ya yi kira ga kwamitin majalisar da su dakatar da duk wani aiki a kan dokar ko kuma su dakatar da duk wani abu da ya shafa dokar da zai hada da ma'aikatansu.

Matsayar ma'aikatar kwadagon sam bata yi wa kwamitin dadi ba don sun jaddada cewa sai sun ci gaba da ji ta kan bukatar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel