Jihohin Yarabawa sun yanke shawarar bude makarantu sabanin umurnin gwamnatin tarayya

Jihohin Yarabawa sun yanke shawarar bude makarantu sabanin umurnin gwamnatin tarayya

Jihohin Kudu maso yamma da akafi sani da yankin kabilar Yoruba 6 sun yanke shawarar bude makarantunsu domin daliban ajin karshen a makarantun sakandare su rubuta jarabawar WAEC wata mai zuwa.

Jihohin sun hada da Lagos, Ogun, Oyo, Ondo, Osun da Ekiti.

Wannan shawara da suka yanke ya sabawa shawaran gwamnatin tarayya inda ta ce ba za'a bude makarantu ba kuma ba za'a rubuta jarabawar WAEC ba bana.

Zaku tuna cewa a makon da ya gabata, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana cewa Najeriya ba zatayi musharaka a jarabawar WAEC ba saboda gudun yaduwar cutar Coronavirus.

Kwamishanonin Ilimi, masu baiwa gwamnoni shawara kan ilimi da shugabannin hukumomin ilimin jihohin sun yanke shawarar hakan ne a ganawar da sukayi ta yanar gizo.

Sun yi ittifaki lallai a bude makarantu a jihohin su bude saboda daliban ajin sakandaren karshe su zana jarabawa.

A jawabin da suka saki bayan ganawar, sun bayyana cewa dalibai su koma makaranta ranar 3 ga watan Agusta, 2020.

Jihohin Yarabawa sun yi yanke shawarar bude makarantu sabanin umurnin gwamnatin tarayya
Jihohin Yarabawa sun yi yanke shawarar bude makarantu sabanin umurnin gwamnatin tarayya
Asali: Facebook

Hakazalika sun yarje zasu garzaya wajen gwamnatin tarayya domin bukatar a daga jarrabawar da makonni uku bayan dawowan dalibai makaranta.

Bayan haka kuma su sake garzayawa wajen hukumar gudanar da jarawabar WAEC domin mika bukatar dage jarawar zuwa ranar 24 ga Agusta.

Wannan ya sha ban-ban da matsayar da jihohin Arewacin Najeriya suka yanke.

Mun kawo muku rahoton cewa kwamishanonin ilimi na jihohi 19 dake Arewacin Najeriya sun bayyana amincewarsu da dakatad da shirin bude makarantu ga daliban azuzuwan karshe da gwamnatin tarayya tayi.

Sun ce ba za'a bude makarantu ba kuma ba za suyi musharaka a jarrabawar WAEC ta bana ba.

Kwamishana ilimin jihar Kaduna, Dakta Shehu Makarfi, wanda shine shugaban kungiyar kwamishanonin ilimin Arewacin Najeriya ya rattaba hannu kan takardar, Punch ta samu.

Kwamishanonin jihohi goma sha uku (13) da suka samu halarta sune na Kaduna, Bauchi, Gombe, Niger, Nasarawa, Adamawa, Taraba, Kogi, Kwara, Katsina, Kano, Borno daJigawa.

Kwamishanonin sun yabawa ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, bisa yanke wannan shawara na hana bude makarantu kuma suna masu mara masa baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel