COVID-19: Gwamna Umahi na jihar Ebonyi zai bude makarantu a watan Agusta

COVID-19: Gwamna Umahi na jihar Ebonyi zai bude makarantu a watan Agusta

- Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya ce jiharsa zata bude makarantu a watan Agusta ko Satumba

- Ya ce amma dole abi matakai kafin bude makarantun, domin gujewa cutar Covid 19

- Umahi ya bukaci al'ummar jihar da su tabbata sun tsaftace makarantunsu kafin zuwan ranar bude makarantun

Gwamnatin jihar Ebonyi ta ce zata bude makarantu a jihar tsakanin watan Agusta da Satumda.

Gwamnan jihar, David Umahi ya bayyana hakan a wani taron majalisar zartaswa na jihar da aka gudanar ta yanar gizo a Abakalaki, babban birnin jihar.

Ya ce za a bude makarantun ne a tsarin mataki mataki.

Ya ce: "Muna son al'umma su sani cewa jihar Ebonyi zata bude makarantunta nan bada jimawa ba, amma ba a watan Yuli ba, dole ne mubi wasu matakai da zasu bamu damar bude makarantun a tsakanin watan Agusta ko Satumba."

"Kuma matakan zasu kasance ne kamar haka, makarantar King David zata fara budewa, ina umurtar dukkanin ko-odinetoci, shuwagabannin kananan hukumomi 13, sarakunan gargagajiya, shuwagabannin kungiyoyi, da su yi amfani da mutane domin gyara dukkanin makarantun sakandire da firamare. Su gyara su tsaf, an jima ana yin hakan, ba wai gwamnati ne kawai zata yi ba.

"Do haka mu gyara makarantun, idan aka yi hakan, ina so kwamishinan ilimi, babban mai bani shawara kan manyan makarantu, su fahimci cewa wannan shine lokacin da za a samar da hanyar karatu ta yanar gizo, ta hanyar farawa da malamai, wannan dama ce ta bunkasa koyarwa ta kafar yanar gizo," a cewarsa.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kashe dan uwan Labaran Maku

COVID-19: Gwamnatin Ebonyi zata bude makarantu a cikin watan Agusta
COVID-19: Gwamnatin Ebonyi zata bude makarantu a cikin watan Agusta
Asali: Depositphotos

Gwamnan ya ce gwamnati zata horas da malamai da dalibai kan matakan da zasu bi domin kare kawuwansu daga kamu da cutar Coronavirus kafin a bude makarantu, yana mai karawa da cewa za a yiwa malamai gwajin cutar.

"Bude makarantu zai fara ne da tsaftace makarantun, duk makarantar da muka gyara, zamu yi mata feshin magani, da kuma yiwa malamanta gwaje gwaje. Haka zalika zamu tura ma'aikatan kiwon lafiya domin ci gaba da wayar da kan al'ummar da ke zaune a inda makarantun suke."

"Idan aka fara karatu zamu horas da malamai domin koyar da yara matakan kariya daga cutar Covid-19, na tswon makon farko na komawa makarantar.

"Wannan cutar ta Covid gaskiya ce kuma dole ne mu bi matakan kariya. Ba wai kawai mu bude makarantu ba, koda ace Nigeria za ta yi asarar shekara daya ta karatu amma kowa zai rayu, to wannan asarar ta cancanta. Makasudin duk wani abu da muke yi shine ci gaban rayuwarmu, don haka ba zamu so yaranmu su koma makaranta ba tare da ilimi kan cutar ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel