Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kashe dan uwan Labaran Maku

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kashe dan uwan Labaran Maku

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu daga jaridar Daily Nigerian na nuni da cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi garkuwa tare da kashe Salisu Usman, dan uwan tsohon ministan watsa labarai, Labaran Maku.

Daily Nigerian ta tattara bayanin cewa 'yan bindigar sun shiga gidan mamacin da ke a garin Gudi, karamar hukumar Akwanga, jihar Nasarawa.

Yan bindigar sun yi awon gaba da Mr. Usman wanda jami'in hukumar shige da fice ne tare da matarsa, inda daga bisani suka kashe su.

KARANTA WANNAN: Karya take yi banci zarafinta ba - Godswill Akpabio ya yiwa Ms. Gbene martani

Da ya ke magana da jaridar The Nation, mahaifin mamacin, ASP Usman Salisu, mai ritaya, ya ce 'yan bindigar sun tsallake katangar gidan kafin suka harbi matar Sa'adatu sau uku ta kofar tagar dakinta.

"Ina a saman teburi ina cin abinci a lokacin da naji karar harbin bindiga na farko da na biyu dana uku, a matsayina na jami'in 'yan sanda, sai na fahimci cewa wadannan 'yan fashi ne. Daga bisani kuma sai na ji 'yayana suna kuka kusa da 'yar uwarsu kwance a cikin jini.

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kashe dan uwan Labaran Maku
Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kashe dan uwan Labaran Maku
Asali: Depositphotos

"Da hanzari na kira wasu abokaina, wadanda tsofaffin ma'aikatan 'yan sanda ne. Amma kafin jami'an 'yan sanda su iso, har 'yan fashin sun kashe diyata, sun kuma yi awon gaba da dana, Usman Salisu, wanda jami'in hukumar shige da fice ne, kafin shima suka kashe shi," a cewar Usman.

Da aka tuntube ta, kwanturolan hukumar shige da fice ta kasa, Zainab Lawal, ta tabbatar da faruwar lamarin.

A wani labarin:

Ministan cin gaban yankin Nigeria Delta, Godswill Akpabio, ya karyata zarginsa da Ms. Gbene Joi Nuneih, tsohuwar manajin darakta na kwamitin kawo gyara na hukumar bunkasa Niger Delta (NDDC), na cewar ya ci zarafin ta.

Ministan, a cikin wata sanarwa da ya bayar a ranar Laraba a Abuja ta hannun Aietie Ekong, hadiminsa ta fuskar watsa labarai, ya ce wannan zargin da ta yi wasa, "karyace kawai tsagoronta".

"Duk kalamanta karairayi ne kawai, babu gaskiya a ciki.

"Ministan bai aikata ba, ko a wani waje, ko a wani lokaci, ko a cikin wani hali, bai ci zarafin Ms. Nunieh, balle ma har ace ya yi yunkurin kamanta wani abu da ya shafi fyade ga Ms. Nunieh, ko kuma wata mace a cikin ma'aikatar ko hukumar NDDC," a cewar sanarwar.

Ms Nunieh, a wata tattaunawa da aka yi da ita a baya bayan nan, ta zargi ministan da cin hanci da rashawa, cin zarafi da kuma muzgunawa ma'aikata, fasa bututun mai, shiga cikin ayyuka kungiyoyin asiri, karya dokokin aikinsa da sauransu.

Ministan Niger Delta, Godswill Akpabio ya karyata zargin cin zarafin Ms. Gbene Source: UGC Amma sanarwar ta jaddada cewa Akpabio bai ci zarafinta ba ta fuskar fyade, kasancewarsa magidanci kuma mai samun gamsuwa daga matarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel