Wata sabuwa: Rikici ya sake barkewa tsakanin sanatoci da ministan Buhari

Wata sabuwa: Rikici ya sake barkewa tsakanin sanatoci da ministan Buhari

Alakar da ke tsakanin ma'aikatar kwadago da majalisar dattawan kasar nan ta sake tabarbarewa a ranar Laraba a yayin da wasu wakilan majalisar da ministan kwadago, Chris Ngige suka samu rashin jituwa.

Rikicin ya fara ne bayan babban darakta a ma'aikatar kwadagon, Eyewumi Neburagho, wanda ya wakilci ministan aka gayyacesa don yin tsokaci a kan wata doka.

Kalamansa sun tada kura bayan da ya bukaci a dakatar da jin ta bakin jama'a tare da dokar har zuwa lokacin da kwamitin majalisar za su gayyaci ma'aikatar tare da tura mata dokar a rubuce.

Neburagho ya musanta cewa, a matsayinsa na daya daga cikin masu ruwa da tsaki, ba a tafiya da ma'aikatarsu a duk lokacin da aka zo jin ta bakin jama'a. Sai dai su turo wakili a duk lokacin da suka samu rahoto daga manema labarai.

Ya ce dole ne ma'aikatar ta san yadda dokar take da kuma yadda za ta shafi ma'aikatanta.

A don haka, ya yi kira ga kwamitin majalisar da su dakatar da duk wani aiki a kan dokar ko kuma su dakatar da duk wani abu da ya shafa dokar da zai hada da ma'aikatansu.

Matsayar ma'aikatar kwadagon sam bata yi wa kwamitin dadi ba don sun jaddada cewa sai sun ci gaba da ji ta kan bukatar.

Shugaban kwamitin, Sanata Uba Sani, ya ja kunnen ma'aikatar da ta guje bai wa majalisar dattawan umarnin yadda za su tafi da al'amuransu.

Ya ce, "Mu 'yan majalisa ne na tarayya kuma an zabe mu ne don yin dokoki a kasar nan. Ba za mu zauna muna kallon wanda aka nada yana fada mana abinda za su yi ba a lokacin da za mu yi."

Wata sabuwa: Rikici ya sake barkewa tsakanin sanatoci da ministan Buhari
Wata sabuwa: Rikici ya sake barkewa tsakanin sanatoci da ministan Buhari. Hoto daga The Punch
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An bi mamallakin kamfani GoKada an kashe har gida

A makon da ya gabata, karamin minsitan kwadago da ayyukan, Festu Keyamo, ya yi musayar yawu da 'yan majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata a kan diban aiki karkashin NDE.

Rikicin ya fara ne a lokacin da darakta janar din NDE, Nasiru Ladan ya kasa kare kasafin kudinsu na N52 biliyan don daukar 'yan Najeriya 774,000 aiki karkashin NDE.

Ministan ya ce an bukaci ma'aikatarsa da ta kula da daukar aikin amma umarni ne daga shugaban kasa Muhammadu Buhari. Lamarin da 'yan majalisar suka musanta tare da soma musayar kalamai da ministan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel