Matar aure ta rabu da mijinta, ta aure dan mijinta

Matar aure ta rabu da mijinta, ta aure dan mijinta

Marina Balmasheva, 'yar asalin kasar Rasha ta aura dan kishiyarta mai shekaru 20 mai suna Vladimir Shavyrin, bayan rabuwarta da mahaifinsa.

Matar mai shekaru 35 ta wallafa bidiyon yadda suka yi auren kotu da dan nata. A halin yanzu, suna tsammanin haihuwa nan ba da dadewa ba, jaridar Daily Mail Online ta ruwaito.

A watan Mayu, Marina mai shekaru 35 ta bayyana labarin a yanar gizo, inda ta wallafa hotunanta tare da Vladimir a lokacin da yake da shekaru 7 a duniya.

Matar aure ta rabu da mijinta, ta aure dan mijinta
Matar aure ta rabu da mijinta, ta aure dan mijinta. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

A ranar aurensu, ta rubuta: "Mun isa wurin daurin auren. Ko gashina ban gyara ba. Zobban duk suna mota. Duk da farin cikin da muke ciki, akwai jin kunya kadan.

"Bayan daurin auren, mun saka kayan biki tare da jin dadinmu a wata liyafa da muka hada a wani gidan cin abinci. A halin yanzu ina da ciki kuma muna son komawa babban birni."

Matar aure ta rabu da mijinta, ta aure dan mijinta
Matar aure ta rabu da mijinta, ta aure dan mijinta. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

Matar 'yar asalin yammacin Krasnodar Krai, na zama da mijinta mai suna Alexey mai shekaru 45 kafin rabuwarsu.

Sun yi zaman aure tun daga 2007 kafin su rabu sannan ta aure dan sa.

Marina ta bayyana cewa basu magana da tsohon mijinta. "Ina tsammanin bai ji dadin abinda muka yi ba," tace.

Matar aure ta rabu da mijinta, ta aure dan mijinta
Matar aure ta rabu da mijinta, ta aure dan mijinta. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matar aure ta kashe aurenta bayan cewa da tayi za ta iya cin amanar mijinta a kan N200,000

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel