Yadda 'yan bindiga suka kashe hakimi a Kebbi

Yadda 'yan bindiga suka kashe hakimi a Kebbi

Kisan da 'yan bindiga suka yi wa Hakimin Bajida na karamar hukumar Fakai ta jihar Kebbi da tsakar rana a makon da ya gabata, ta jefa al'umma cikin dimuwa.

'Yan bindiga sun kashe Alhaji Musa Muhammad Bahago, yayin da ya ke kan hanyarsa ta dawo wa daga garin Zuru.

Wani makusancinsa ya shaidawa manema labarai cewa, kwanaki kadan gabanin hakan ta faru, wasu 'yan bindiga kimanin 20 sun dira a fadarsa rike da bindigu su na tambayar inda yake.

An ruwaito cewa, 'yan binidgar sun iso fadar ne haye a kan babura takwas kuma a kan kowane babur akwai mutum daya da ke sanye da takunkumin rufe fuska.

Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya; Muhammad Adamu
Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya; Muhammad Adamu
Asali: Facebook

Bayan sun gama lalube fadarsa, 'yan bindigar sun kama gabansu cikin fushi na rashin riskar wanda suka zo nema.

A yayin da marigayi Bahago ya samu labarin cewa akwai masu neman hallaka shi, ya yi gaggawar shigar da kara ga magabatansa da sauran 'yan uwansa masarauta.

Sun shawarce shi a kan ya takaice duk wasu tafiye-tafiyensa matukar ba su zama dole ba.

Sai dai da ya ke tsautsayi ba ya wuce ranarsa, Marigayi Bahago ya bar garin Zuru domin shaidawa jami'an 'yan sandan cewa rayuwarsa tana cikin hadari, ashe masu neman ganin bayansa sun labe suna hakon duk wani motsinsa.

Marigayi Bahago wanda ya dade ba ya fita domin daukan shawarar 'yan uwansa masarauta, ya kama hanyar Zuru shi kadai domin gudun daukan hankalin mutane.

KARANTA KUMA: Ganduje ya naɗa sabon kwamishina a jihar Kano

Maharan sun datse hanyarsa da misalin karfi 4.00 na Yamma inda suka sassara shi da adduna kuma suka kama gabansu inda ya mutu nan take.

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kebbi, ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari.

Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa, har kawo yanzu babu mutum ko guda da ake zargi da aikata wannan mummunar ta'ada da ya shiga hannu.

Sai dai ya bayar da tabbacin cewa, jami'an hukumar ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da tsananta bincike domin ganin wadanda suka aikata wannan ta'adda sun fuskanci hukunci daidai da abinda suka aikata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel