Karya take yi banci zarafinta ba - Godswill Akpabio ya yiwa Ms. Gbene martani

Karya take yi banci zarafinta ba - Godswill Akpabio ya yiwa Ms. Gbene martani

- Ministan ma'aikatar Niger Delta, Godswill Akpabio ya karyata zargin cin zarafin Ms. Gbene

- Ya bayyana cewa yana da matarsa wacce kuma har sun haifi yara mata hudu, don haka babu dalilin da zaisa ya yi yunkurin cin zarafin Ms. Gbene

- Haka zalika ya yi ikirarin cewa Ms. Gbene ta kunna wutar ne don cimma burinta da kuma burin wadanda suke daukar nauyinta

Ministan cin gaban yankin Nigeria Delta, Godswill Akpabio, ya karyata zarginsa da Ms. Gbene Joi Nuneih, tsohuwar manajin darakta na kwamitin kawo gyara na hukumar bunkasa Niger Delta (NDDC), na cewar ya ci zarafin ta.

Ministan, a cikin wata sanarwa da ya bayar a ranar Laraba a Abuja ta hannun Aietie Ekong, hadiminsa ta fuskar watsa labarai, ya ce wannan zargin da ta yi wasa, "karyace kawai tsagoronta".

"Duk kalamanta karairayi ne kawai, babu gaskiya a ciki.

"Ministan bai aikata ba, ko a wani waje, ko a wani lokaci, ko a cikin wani hali, bai ci zarafin Ms. Nunieh, balle ma har ace ya yi yunkurin kamanta wani abu da ya shafi fyade ga Ms. Nunieh, ko kuma wata mace a cikin ma'aikatar ko hukumar NDDC," a cewar sanarwar.

Ms Nunieh, a wata tattaunawa da aka yi da ita a baya bayan nan, ta zargi ministan da cin hanci da rashawa, cin zarafi da kuma muzgunawa ma'aikata, fasa bututun mai, shiga cikin ayyuka kungiyoyin asiri, karya dokokin aikinsa da sauransu.

KARANTA WANNAN: Handame N1.5bn: Kotu ta daure tsohon shugaban hukumar NIMASA shekaru 7 a gidan kaso

Ministan Niger Delta, Godswill Akpabio ya karyata zargin cin zarafin Ms. Gbene
Ministan Niger Delta, Godswill Akpabio ya karyata zargin cin zarafin Ms. Gbene
Asali: UGC

Amma sanarwar ta jaddada cewa Akpabio bai ci zarafinta ba ta fuskar fyade, kasancewarsa magidanci kuma mai samun gamsuwa daga matarsa.

"A yanzu haka shida iyalinsa, sun haifi yara guda hudu wadanda dukansu matane da ke tasowa," a cewar sanarwar.

Akpabio ya ce ya zamar masa wajibi ya fito ya kare kansa akan wannan zargi saboda gwamnatinsa da kuma kishin da yake yiwa matarsa, Mrs. Ekaete Akpabio, 'yayansa da kuma 'yan uwansa.

A cewar sanarwar: "A domin haka, ministan, ya kalli wannan zargi a matsayin batancin suna da kuma yunkurin amfani da hakan don zama karen farauta ga Ms. Nunieh, na cewar wai ya gabaceta da yunkurin cin zarafinta, a lokacin da ta ke mukamin manajan darakta na hukumar NDDC.

"Ministan ya kuma yi mamaki matuka kan yadda Ms. Nunieh ta gaza kai karar lamarin ga rundunar 'yan sanda a lokacin da lamarin ya auku, kafin ta bar aikinta a ranar 17 ga watan Fabreru, 2020, idan har zargin nata da gaske ne.

"Amma shine ta jira har sai ranar 10 da kuma ranar 13 ga watan Yulin 2020 a lokacin da majalisar tarayya ke bincikar wasu daga cikin ayyukan da ta gudanar a matsayinta na manajan darakta na IMC, musamman a yanzu da binciken kudade ya fara zafi a hukumar NDDC, lokacin da kowa ya zura idanuwa don ganin gaskiyar badakalar da aka yi."

Ministan ya ce wannan wuta da Ms. Nunieh ta kunno tayi su ne kawai domin cimma muradun kanta da kuma cimma muradun wasu da ke daukar nauyinta, yana mai cewa wadanda ke jin tsoron gaskiya ne kawai zasu so kada a yi 'yan tone tone.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel