Ganduje ya naɗa sabon kwamishina a jihar Kano
A yau Laraba, 15 ga watan Yuli, gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya rantsar da sabon kwamishina, Idris Garba Unguwar Rimi, wanda zai kasance ɗaya daga cikin 'yan majalisar zartarwa na gwamnatin jihar.
A yayin rantsar da Idris Garba, Ganduje ya ce wannan sabon naɗi ya biyo bayan gibin da aka samu a majalisar zartarwa ta gwamnatinsa bayan tsige wani kwamishina da ya yi a kwanakin baya.
Kamar yadda Gidan Rediyon Freedom mai tushe a Kano ya ruwaito, Ganduje ya ce zuwa gaba za a fayyace ma'aikatar da sabon kwamishinan zai jagoranta.
A nasa jawaban, sabon kwamishinan da ake dakon jin ma'aikatar da za a mika masa akalar jagorancinta, ya ce tun a yanzu ya daura damarar tabbatar da ci gaban jihar Kano.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Rahotanni sun bayyana cewa, sabon kwamishinan shi ne tsohon shugaban karamar hukumar Tofa kuma tsohon kwamishinan kimiya da fasaha na jihar.
Ana iya tuna cewa, watanni biyu da suka gabata ne Gwamna Ganduje ya tube kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Mu'azu Magaji Dan Sarauniya.
KARANTA KUMA: Na yi baƙin cikin rasuwar mahaifiyar hadimi na - Atiku
Gwamnan Kano ya tsige Dan Sarauniya daga mukaminsa bayan wasu kalamai da ya wallafa kan shafinsa na dandalin sada zumunta, wato 'facebook', a kan mutuwar Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.
Jama'a da dama sun fassara wallafar da Injinya Magaji ya yi a matsayin nuna murna da mutuwar Kyari, lamarin da ya sa har Gwamna Ganduje ya sallame shi jim kadan bayan wallafa rubutun.
Sai dai, a wani jawabin da tsohon kwamishinan ya fitar, ya ce an yi wa rubutunsa mummunar fassara tare da bayyana cewar shi ba murnar mutuwar Kyari ya ke yi ba.
A cikin jawabin, Magaji ya bayyana cewa babu yadda za a yi a matsayinsa na Musulmi ya yi murnar mutuwar ɗan uwansa musulmi ko ma wani mutumin da ba musulmi ba.
A wani rahoto da Legit.ng ta ruwaito, a makon jiya ne Ganduje ya aike wa da Majalisar dokokin Jihar sunayen kwamishinoni uku da ya zaba domin neman amincewarta.
Kakakin Majalisar, Abdulazeez Gafasa ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar na ranar Talata 7 ga watan Yulin 2020.
Gafasa ya ce gwamnan na neman amincewar majalisar domin nada Idris Garba a matsayin kwamishina kuma mamba na majalisar zartarwa ta Jihar, SEC.
Ya ce gwamnan ya kuma nemi 'yan majalisar su tabbatar da nadin wasu kwamishinoni biyu a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na jihar, KANSIEC.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng