Na yi baƙin cikin rasuwar mahaifiyar hadimi na - Atiku

Na yi baƙin cikin rasuwar mahaifiyar hadimi na - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi alhini tare da jimamin mutuwar mahaifiyar wani hadiminsa, Yahaya Ibrahim Zango.

Yahaya Zango shi ne hadimi na musamman kuma babban mashawarci kan harkokin gudanarwa a Jami'ar Amurka ta Najeriya wadda Atiku ya mallaka.

Atiku ya yi ta'aziyar mutuwar Hajiya Fatima Ibrahim Tafida Zango, a wani sako da ya wallafa kan shafinsa na Twitter da misalin karfe 7.45 na Yammacin ranar Talata, 15 ga watan Yuli.

A sakon da Atiku ya wallafa, ya bayyana cewa, ya yi baƙin cikin rasuwar mahaifiyar hadimin nasa tare da bayyana yadda mutuwar ta girgiza shi.

Atiku Abubakar
Hoto daga; Nairametrics
Atiku Abubakar Hoto daga; Nairametrics
Asali: UGC

Wazirin na Adamawa ya yi addu'a ta rokon Mai Duka ya jikanta da Rahama, tare da neman Ya yafe mata kurarenta. Ya kuma yi addu'ar Allah ya sa Aljannar Firdausi ce makomarta.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, rundunar sojin saman Najeriya (NAF), ta sanar da mummunan labari na mutuwar matukiyar jirgin yakinta mace ta farko, Tolulope Arotile.

Mutuwar Tolutope ta zo ne watanni takwas bayan rundunar sojin saman ta yi mata karramawa ta musamman.

KARANTA KUMA: Muƙamai da albashin ma'aikatan 'yan sanda a Najeriya

NAF ce ta sanar da labarin mutuwar Arotile, wanda aka bayyana a matsayin abun “takaici” a cikin wani jawabi da ta fitar a ranar Talata, 14 ga watan Yuli.

An tattaro cewa hazikar sojan ta rasu ne sakamakon wani hatsarin mota da ya auku a jihar Kaduna.

Matashiyar mai shekaru 23 a duniya ta amsa kiran Mahaliccinta bayan ta samu wasu raunuka a ka sanadiyar hatsarin da ya afku a sansanin NAF dake Kaduna.

"Cike da tarin nauyin zuciya rundunar sojin saman Najeriya na bakin cikin sanar da mutuwar matukiyar jirginta Tolulope Arotile, wacce ta mutu a ranar 14 ga watan Yuli 2020, sakamakon raunukan da ta samu a kai daga hatsarin mota a sansanin sojin sama a Kaduna.

Har zuwa mutuwarta, Fg Offr Arotile, wacce aka kaddamar cikin NAF a watan Satumban 2017 a matsayin mamba ta makarantar horas da dakaru wato Nigeria Defence Academy RC 64, ta kasance matukiyar jirgin yaki ta farko a hukumar," cewar wani bangare na jawabin

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel