Da duminsa: Buhari na jagorantar zaman majalisar zartaswa a fadar Aso Villa (Hotuna)

Da duminsa: Buhari na jagorantar zaman majalisar zartaswa a fadar Aso Villa (Hotuna)

- Buhari ya jagoranci zaman majalisar zantarwa karo na shida ana kiyaye dokar nesa-nesa da juna

- Ministoci sun halarci zaman majalisar da shugaba Buhari ya jagoranta a yau Laraba

A yau Laraba, 15 ga watan Yuli, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara jagorantar zaman majalisar zartarwa a fadar gwamnatinsa ta Aso Villa da ke babban birnin Tarayya Abuja.

Wannan shi zaman majalisar na bakwai da shugaban kasar ya jagoranta da aka kiyaye dokar nesa-nesa da juna inda ta hanyar amfani da yanar gizo wajen tattaunawa.

Ministocin da a dole su na da ta cewa kuma su na dauke da bayanan da za su gabatar su ne kadai suka halarci zaman majalisar a fadar shugaban kasa.

Daga cikin wadanda ke hallare akwai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari.

Saura sune ministan shari'a, Abubakar Malami, da ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmed.

Gabanin fara tattaunawa kan al'amuran da suka shafi zaman majalisar na yau, shugaba Buhari ya nemi da a yi shiru na minti daya domin yin alhinin mutuwar tsohon ministan ayyuka, John Obada.

KU KARANTA: Hukumar kula da tashoshin jirgin sama ta yi Alla-wadai da tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari

Da duminsa: Buhari na jagorantar zaman majalisar zartaswa a fadar Aso Villa (Hotuna)
Da duminsa: Buhari na jagorantar zaman majalisar zartaswa a fadar Aso Villa (Hotuna)
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel