Kudin horar da Jami'ai: An titsiye Magu kan N700m da ta ɓata a hukumar EFCC

Kudin horar da Jami'ai: An titsiye Magu kan N700m da ta ɓata a hukumar EFCC

Tun a ranar Talata 7 ga watan Yuli, fadar shugaban kasa ta dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati.

Hakan ya biyo bayan bayyanar da Magu ya yi a gaban kwamitin da fadar shugaban kasar ta kafa domin bincike kan zargin da ake yi masa na yin sama da fadi da dukiyar gwamnati.

Magu ya bayyana a gaban kwamitin, wanda tsohon shugaban kotun daukaka kara, Mai shari'a Ayo Salami ke jagoranta.

Kwamitin ya gayyaci Magu ne domin jin ta bakinsa da kuma neman ya wanke kansa daga zargin yin ruf da ciki kan dukiyar kasa da kuma cin amanar kujerarsa.

Ibrahim Magu
Hoto daga Premium Times
Ibrahim Magu Hoto daga Premium Times
Asali: UGC

Kawo yau Laraba, kwanaki bakwai kenan kwamitin na ci gaba da titsiye Magu da tatso bayanai domin tabbatar da zargin da ake masa.

A Talatar da ta gabata ne Magu a karo na shida, ya sake bayyana a gaban kwamitin domin amsa tambayoyin kan laifukan da ministan shari'a, Abubakar Malami ya ke tuhumarsa da aikata wa.

A yayin binciken, kwamitin ya nemi Magu ya yi bayani kan naira miliyan 700 da hukumar EFCC ta fitar domin horas da jami'anta, bayan kuma ba a gudanar da wannan horo ba.

KARANTA KUMA: Yadda kwamitin bincike ya taso keyar wasu manyan Jami’an Hukumar EFCC

Wata majiyar rahoto ta bayyana cewa, a yayin binciken, kwamitin ya karbe wasu motoci uku marasa jin harbin harsashi daga hannun dakataccen shugaban na EFCC.

Daya daga cikin motocin an samo ta ne a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Haka kuma, wasu daga cikin mambobin kwamitin, sun garzaya hedikwatar hukumar EFCC, inda suka taso keyar wasu manyan jami'ai uku na hukumar da kuma wasu kwamfutoci.

Daga cikin wadanda lambarsu ta fito har da wani tsohon kwamishinan 'yan sanda, Mohammed Umar wanda ya kasance darektan gudanarwa a lokacin da Magu ya ke rike da shugabancin hukumar.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, jami'an uku an waresu a wuri daban da wurin da aka girke Magu inda yake amsa tambayoyi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng