Bayan lalata yara maza 3, kotun Kano ta yankewa Katon dan luwadi daurin shekaru 2 kacal
Wata kotun Majistare dake zanne a jihar Kano ranar Talata ta yankewa wani matashi dan shekara 30, Umar AbdulRahman , hukuncin daurin watanni 24 a gidaN gyara hali kan laifin lalata kananan yara maza uku.
Kotun ta kama AbdulRahman, wanda mazaunin Layin Yankifi Maidile Quarters ne a Kano, da laifin aikata ba daidai ba.
Alkalin kotun Majistaren, Muhammad Idris, ya yanke mai hukuncin daurin shekaru biyu kuma babu damar beli.
Lauyan gwamnati, Badamasi Gawuna, ya bayyanawa kotu cewa iyayen Umar Tanko da Ahmad Bello, dukkansu mazauna Mundadu Quarters sun shigar da kara ofishin yan sandan Kumbotso ranar 23 ga Afrilu.
Ya ce Umaru AbdulRahman ya yi lalata da kananan uku, sannan ya baiwa kowanne cikinsu N50.
Ya ce hakan ya sabawa sashe 284 na dokar Penal Code.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Za mu kaddamar da bincike kan yadda Sojoji 365 suka ajiye aiki - Majalisa
A wani labari mai kama da haka, a ranar Talata, wata kotun Majistare da ke Kano,ta ba da umarnin garkame wani mutum mai shekaru 55, Abdullahi Haladu, a gidan gyara hali na Goron Dutse, bisa zargin yi wa yarinya ‘yar shekara 7 fyade.
Mutumin wanda ake zargi da aikata wannan mummunan laifi da ya saba wa sashe na 283 na final kot, mazauni ne a Unguwar Mahauta ta kauyen Gani da ke jihar Kano.
Jami'in dan sanda mai shigar da kara, ASP Badamasi Gawuna, ya shaidawa kotun cewa, wani mutum mai suna Isa Uba, shi ne ya yi karar Haladu a ofishin 'yan sanda na Sumaila a ranar 29 ga watan Yuni.
Mallam Uba wanda shi ma mazauni ne a Unguwar Mahauta, ya yi ikirarin cewa, wanda ake zargi ya aikata laifin ne da misalin karfe 8.00 na dare, inda ya yi amfani da hikima wajen shigar da yarinyar dakinsa kuma ya aikata masha'a da ita.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng