Harin Borno: Rundunar 'yan sanda ta ceto sojoji 2 daga hannun Boko Haram

Harin Borno: Rundunar 'yan sanda ta ceto sojoji 2 daga hannun Boko Haram

- Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar ceto wasu sojoji guda biyu da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su

- Sai da jami'an rundunar 'yan sandan sun yi bata kashi da 'yan ta'addan kafin suka samu nasarar kwato sojojin

- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun yi kokarin kwace barikin soji na runduna ta 333 amma hakan bai yiyu ba

Rundunar 'yan sanda karkashin sashen dakile ta'addanci ta samu nasarar ceto wasu sojoji guda biyu da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su bayan da suka kai wani hari a jihar Borno.

A cikin wani rahoto na 'al'amarin da ke faruwa'. SITREP, da jaridar PRNigeria ta samu, ya bayyana cewa jami'an rundunar 'yan sandan sun yi bata kashi da 'yan ta'addan kafin suka samu nasarar kwato sojojin.

"Da misalin karfe 2:00 na ranar 13 ga watan Yulin 2020, mayakan kungiyar Boko Haram sun kai farmaki wa tawagar tsaro ta rundunar soji akan hanyar Auno, inda suka kashe sojoji biyu tare da sace wasu, yayin da suka yi awon gaba da bindigogi guda biyu kirar AK 47 mallakin sojojin da kuma harsasai masu yawa.

"Sashen dakile ta'addanci na rundunar 'yan sanda sun samu damar gudanar da bin sahun 'yan ta'addan, inda suka yi musayar wuta, a karshe suka kwato bindiga guda daya da harsasai, sannan suka samu nasarar kubutar da sojoji guda biyu da ransu.

KARANTA WANNAN: Gwamna Abdulrazaq ya bukaci EFCC ta binciki kudaden kananan hukumomin jiharsa

"Dukkanin abubuwan da aka kwato an mikasu a hannun hukumar rundunar 'yan sandan," cewar rahoton tsaron.

Harin Borno: Rundunar 'yan sanda ta ceto sojoji 2 daga hannun Boko Haram
Harin Borno: Rundunar 'yan sanda ta ceto sojoji 2 daga hannun Boko Haram
Asali: Depositphotos

A wani labarin makamancin wannan, rundunar tsaron Nigeria sun samu nasarar dakile wani harin mayakan Boko Haram na yunkurin kwace sansanonin rundunar soji a Maiduguri.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun yi kokarin kwace barikin soji na runduna ta 333 amma hakan bai yiyu ba, bayan da akayi musayar wuta na tsawon awanni biyu, tsakanin daren ranar Litinin da asubahin ranar Talata.

Idan ba a manta ba, rahotanni sun bayyana cewa a ranar Talatar da ta gabata mayakan Boko Haram suka kai harin sunkuru ga rundunar soji da ke ran-gadi akan titin Maiduguri-Damboa, a jihar Borno.

Harin, ya jawo asarar rayukan sojoji, kamar yadda jaridar The Sun da Daily Trust suka ruwaito, yayin da mayakan Boko Haram din suka yi garkuwa da wasu sojojin tare da tafiya da bindigoginsu kirar AK 47 da harsasai masu yawa.

"Cikin jimami, na ke sanar da ku cewa mun rasa sojoji guda biyu, yayin da sojoji hudu suka jikkata," cewar Manjo Janar John Enenche, wani mai magana da yawun rundunar.

Ya ce rundunar sojin ta samu nasarar kashe 'yan ta'adda 17 tare da jikkata da dama daga cikinsu.

Tun bayan da ta kaddamar da harinta na farko a jihohin Arewa maso Gabas a shekarar 2009, Boko Haram ta ci gaba da kai hare hare ga jami'an tsaro da kuma fararen hula a yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel