Za mu kaddamar da bincike kan yadda Sojoji 365 suka ajiye aiki - Majalisa

Za mu kaddamar da bincike kan yadda Sojoji 365 suka ajiye aiki - Majalisa

Majalisar wakilan tarayya ta yanke shawarar kaddamar da bincike kan lamarin da ya kai ga jami'an Sojoji 365 sukayi murabus daga aikin Soja dare daya.

Yan majalisan sun yanke hakan ne bisa kudirin kar ta kwanar da mai tsawatarwa a majalisar, Mohammed Monguno, ya shigar a zauren majalisa ranar Talata.

Yayin gabatar da kudirin, Monguno ya a ranar 22 ga Yuni, 2020, wani jami'in Soji, Martin Idakpeni, ya yi jawabi a faifan bidiyo inda ya caccaki babban hafsan Soji kan yadda ake yiwa Sojoji kisa kiyashi.

Ya ce Sojan ya nuna bacin ransa kan irin halin kakaniyen da Sojoji da ciki musamman wadanda ke faggen fama.

A cewarsa, lokuta da dama Sojoji sun saba umurnin manyansu saboda rashin kula da cin zarafi da ake musu.

Hakazalika sau da dama an samu kananan Sojoji sun yi kokarin kashe manyansu saboda irin rashin adalci da suke musu.

KU KARANTA: Bayan lalata yara maza 3, kotun Kano ta yankewa Katon dan luwadi daurin shekaru 2 kacal

Za mu kaddamar da bincike kan yadda Sojoji 365 suka ajiye aiki - Majalisa
Za mu kaddamar da bincike kan yadda Sojoji 365 suka ajiye aiki - Majalisa
Asali: UGC

A ranar Asabar, mun kawo muku rahoton cewa da alamun abubuwa sun fara tabarbarewa matsalar rashin tsaro a kasar nan yayinda Sojojin Najeriya dari uku da hamsin da shida (356) suka ajiye aikin Soja bisa dalili na gajiya da aikin.

Rahoto daga Premium Times ya nuna cewa da yawa cikin Sojojin da sukayi murabus daga aikin Soja sun kasance wadanda ke yakin Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya.

Akwai wasu kuma dake aiki a wasu yankunan daban.

A yanzu dai hukumar Sojin Najeriya na fuskantar barazana a dukkan yankunan Arewacin Najeriya.

Yayinda ake fama da yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso gabas, ana fama da yan bindiga da garkuwa da mutane a Arewa maso yamma, sannan rikicin makiyaya da manoma a tsakiya.

Amma sabanin Soji 356 da sukayi murabus sakamakon gajiya da aiki, wasu 24 daban sun yi ritaya saboda son karbar sarauta a kauyukansu, jimillan Soji 380 kenan, majiyar PT ya bayyana.

A karshe, kakakin majalisa dokokin, Femi Gbajabiamila, ya baiwa kwamitin hukumar Soji majalisar aikin kaddamar da bincike cikin makon daya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel