Raɗaɗin ciwo ya sa wani mutum ya feɗe cikinsa da wuƙa a Kaduna

Raɗaɗin ciwo ya sa wani mutum ya feɗe cikinsa da wuƙa a Kaduna

Sakamakon raɗaɗin ciwo na gyambon ciki wato Ulcer da ya addabi wani magidanci, ya sanya mutumin ya feɗe cikinsa da wuƙa a Kaduna dake Arewacin Najeriya.

Gidan Rediyon Freedom mai tushe a jihar Kano ya ruwaito cewa, wannan abun al'ajabi ya faru ne a garin Lere da ke Kudancin jihar ta Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa, raɗaɗin ciwo na gyambon ciki ya sanya Hashimu Muhammad ya yi amfani da wata 'yar karamar zabira wajen buɗe cikinsa ko zai ɗan samu sa'ida.

A yayin tattaunawa da wata ƙanwar Hashimu, ta bayar da shaidar cewa, ɗan uwan nata ya daɗe yana fama da cutar gyambon ciki, sai dai fa a wannan karo lamarin ya ƙara tsananta.

Raɗaɗin ciwo ya sa wani mutum ya feɗe cikinsa da wuƙa a Kaduna
Hakkin mallakar hoto; Freedom Radio
Raɗaɗin ciwo ya sa wani mutum ya feɗe cikinsa da wuƙa a Kaduna Hakkin mallakar hoto; Freedom Radio
Asali: Twitter

Wakilin Gidan Rediyon Freedom Haruna Ibrahim Idris, ya ce a halin yanzu Hashimu yana can yana fama da jinya a babban asibitin garin Lere cikin mawuyacin hali karkashin kulawar mahukunta lafiya.

A wani rahoto da jaridar Legit.ng ta ruwaito, wata yarinya 'yar shekaru 14 mai suna Anita Haledu Ibrahim, ta kashe kanta bayan ta dauko cikin shege.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Anita daliba ce a makarantar gwamnati ta kimiyya da ke Andaha kusa da Akwanga.

Ta sha maganin kashe kwari don sawwake kanta a ranar Asabar, 11 ga watan Yulin 2020.

Kamar yadda majiyoyi suka sanar, saurayin Anita ne ya dirka mata ciki bayan haduwarsu a Andaha yayin kullen korona.

Sun shaku har ta samu ciki amma daga baya sai ta koma kauyensu da ke Abuja.

KARANTA KUMA: Kano: Kotu ta garkame mutumin da ake zargi da yiwa wata yarinya ‘yar shekara 7 fyade

Bayan iyayenta sun tuntubi saurayin, ya amsa cewa cikinsa ne kuma ya bayyana bukatar aurenta.

Anita ta yanke hukuncin kashe kanta bayan mahaifinta, Haledu Ibrahim, ya yi mata mugun duka a kan cikin.

Bayan ta labe ta sha maganin kashe kwarin, an yi gaggawar kai ta asibiti inda ta ce ga garinku nan a ranar Talata, 14 ga watan Yuli.

A halin yanzu 'yan uwanta a can sun fara shirye-shiryen gudanar da jana'izarta tare da sanya ta a makwancin karshe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel