Ma'aikatan EFCC sun kare Magu a kan wata tuhuma daya da ake masa

Ma'aikatan EFCC sun kare Magu a kan wata tuhuma daya da ake masa

Kudaden da hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta kwato daga hannun mabarnata ana ajiyesu ne a babban bankin kasa (CBN), a cewar tsofin ma'aikatan EFCC da kuma ma'aikatan hukumar na yanzu.

Lauyan Magu ya ce ba a adana kudaden da aka kwace a asusun samun riba, kamar yadda ake zargin cewa Magu ya wawure ribar da ake samu a kan kudaden da aka adana bayan kwacesu daga hannun barayin gwamnati.

A ranar Lahadi ne kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa wani bangare na rahoton kwamitin bincike da shugaban kasa ya kafa ya yi zargin cewa Magu ya barnatar da ribar da aka samu sakamakon ajiye kudaden da aka kwato a banki.

Kwamitin, wanda aka kafa domin bin kwakwafi da kwato kadarori (PCARA), ya bayyana hakan ne a cikin wani bangare na rahoton sakamakon bincike Magu da ya fada hannun 'yan jaridu.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ne ya kafa kwamitin PCARA a shekarar 2015.

Ma'aikatan EFCC sun kare Magu a kan wata tuhuma daya da ake masa
Ibrahim Magu
Asali: UGC

Tsohon shugaban kotunan daukaka kara, Jastis Isa Ayo Salami, ne yake jagorantar kwamitin PCARA.

An shigo cikin mako na biyu da fara binciken Magu bisa zarginsa da almundahana da kuma rashin biyayya, kamar yadda ministan shari'a, Abubakar Malami, ya yi korafi a kansa.

Tun ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, da Magu ya fara gurfana a gaban kwamitin, har yanzu ba a bayar da belinsa ba.

Sai dai, tsofin maikata da masu aiki yanzu haka a hukumar EFCC sun yi watsi da zargin da ake yi wa Magu a kan cewa ya wawure ribar da kudaden suka samar sakamakon ajiyesu a asusun banki na musamman.

DUBA WANNAN: Jami'an 'yan sanda 7 sun rasa ransu a hanyar zuwa jihar Katsina

Sun bayyana cewa ba a adana kudaden a wani asusu a wani banki bayan asusun gwamnatin tarayya da ke babban bankin kasa (CBN).

A ranar Litinin ne jaridar Daily Trus ta wallafa cewa babban akanta na kasa (AGF), Ahmed Idris, ya tabbatar da cewa ba a samun kowacce riba daga kudaden da ake sakawa a asusun bai daya na gwamnatin tarayya (TSA).

Wahab Shitu, lauya mai kare Magu, ya ce karyace kawai da sharri ake yi wa Magu dangane da batun samun wata riba daga kudaden da EFCC ta kwace, ta saka a aljihun gwamnatn tarayya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel