Ziyara kawai na kaiwa Magu Dubai, ban amshi N573m hannunsa ba - Fasto

Ziyara kawai na kaiwa Magu Dubai, ban amshi N573m hannunsa ba - Fasto

Jagoran cocin Divine Hand of God Prophetic Ministries Abuja, Emmanuel Omale, ya barranta kansa da rahoton cewa ya amshi kudi hannun shugaban hukumar EFCC da aka dakatar, Ibrahim Magu.

Omale ya karyata rahoton cewa ya sayi dukiyan N573m a Dubai a madadin shugaban hukumar yaki da rashawar dake gurfana gaban kwamitin bincike a halin yanzu.

Ya bayyana hakan ne a wasikar da lauyansa, Gordy Uche, ya aikewa kamfanin dillancin labarai a Najeriya NAN ranar Litinin.

Malamin addinin ya ce ziyara kawai ya kaiwa Magu a Dubai, kasar UAE a watan Maris na 2020.

A cewar Fasto Omale, Magu na zuwa cocinsa Ibada.

Lauyan Faston yace: "Abokin harkallanmu bai taba rikewa Ibrahim Magu wani kudi ba. Bai da wani asusun banki a kasar waje ko wani waje a duniya. hakazalika bai da wani dukiya a Dubai."

"Ba'a taba amfani da sunansa wajen sayen dukiyoyi a Dubai ko wani kasa a duniya ba, hakazalika bai sayawa Ibrahim Magu dukiya a wata kasa a duniya ba."

Ya bukaci kamfanin dillancin labarai a Najeriya NAN ta janye rahotonta kuma ta wallafa wasikar neman afuwarsa cikin jaridu uku daban-daban cikin kwanaki bakwai ko ya shigar da su kara kotu.

Ziyara kawai na kaiwa Magu Dubai, ban amshi N573m hannunsa ba - Fasto
Fasto Omale
Asali: Facebook

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel