Likitoci 35 sun kamu da cutar COVID-19 a jihar Kwara - NMA

Likitoci 35 sun kamu da cutar COVID-19 a jihar Kwara - NMA

- Akalla likitoci 35 sun kamu da cutar COVID-19 a jihar Kwara

- Shugaban kungiyar NMA na jihar Dr. Kolade Solagberu ya roki al'umma da su gujewa shiga cinkoso ko kai ziyara asibitoci

- Ya zuwa ranar Litinin, jihar Kwara na da sama da mutane 401 da suka kamu da cutar Coronavirus inda 14 suka mutu

Rahotannin da aka tattara a ranar Litinin na nuni da cewa akalla likitoci 35 ne suka kamu da cutar COVID-19 a jihar Kwara.

Shugaban kungiyar likitocin Nigeria (NMA) reshen jihar, Dr. Kolade Solagberu ya shaidawa manema labarai a Ilorin, babban birnin jihar, a taron shekara shekara na kungiyar da suke gudanarwa.

Dr. Solagberu, ya ce har zuwa yanzu babu wata babbar illa da cutar ta yiwa mambobinta, domin ba a rasa ran kowa ba.

Shugaban kungiyar NMA ya shaidawa mazauna jihar cewa cutar COVID-19 gaskiya ce; yana mai bukatar su dasu gujewa jita jita na cewar an kirkiro cutar ne domin gwamnati ta samu kudaden shiga.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Kotun koli ta kori karar Lagos da Ekiti na haramta zaman kotu a yanar gizo

A cewarsa: "Ya kamata al'ummar jihar su taimakawa likitoci wajen kauracewa kai ziyarta barkatai ga asibitoci da wuraren cinkoso."

Ya kuma jinjinawa gwamnatin tarayya da ta jiha bisa dogewarsu na kulle makarantu, yana mai karawa da cewa kula da lafiya yafi neman magani.

Likitoci 35 sun kamu da cutar COVID-19 a jihar Kwara - NMA
Likitoci 35 sun kamu da cutar COVID-19 a jihar Kwara - NMA
Asali: Twitter

Ya zuwa ranar Litinin, jihar Kwara na da sama da mutane 401 da suka kamu da cutar Coronavirus, inda aka sallami 179, yayin da har yanzu mutane 208 ke dauke da cutar, inda 14 suka mutu.

A kwanakin bayane Legit.ng ta wallafa rahoton cewa wasu likitoci 10 a Kano sun kamu da kwayar cutar covid-19 yayin da su ke aikinsu na kula da lafiyar jama'a.

Shugaban kungiyar likitocin da ke aiki a asibitin koyarwa na AKTH da ke Kano, Dakta Abubakar Nagoma, ya ce marasa lafiya da ke ziyartar asibitin ba sa son fadin gaskiya yayin bayar da bayanansu.

Ya shaidawa manema labarai cewa ma'aikatan lafiyar sun kamu da kwayar cutar ne yayin da su ke kan aikinsu, ya kara da cewa daga cikin ma'aikatan lafiyar akwai manyan likitoci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel