A lokacin da nake shugaban kasa ban bi son kaina ba - Obasanjo

A lokacin da nake shugaban kasa ban bi son kaina ba - Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya magantu a kan akidar da ya rika yi yayin da ya ke juya akalar jagorancin kasar a matsayinsa na shugaban kasa.

Obasanjo ya bayyana cewa duk wani hukunci da mataki da ya dauka a lokacin da yake shugaban kasa, ya yi shi ne da manufar tabbatar da ci gaban kasar nan da kuma bunkasarta.

Tsohon shugaban kasar ya ce ko kadan bai damu da son kansa ba a yayin da mulki kasar nan a tsawon shekaru takwas daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Ya ce masu ikirarin cewa bai yi wa Yarbawa ko yankin Kudu maso Yammacin kasar komai ba, sun fadi ba daidai ba.

Dattijon kasar ya ce duk masu babatu da cewa bai tsinana komai ba ga yankinsa na Kudu maso Yamma ba ko kuma 'yan kabilarsa ta Yarbawa, ba su san me suke fadi ba.

Obasanjo da shugaba Muhammadu Buhari
Obasanjo da shugaba Muhammadu Buhari
Asali: Twitter

Obasanjo ya yi wannan furuci ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai na jaridar The Point a ranar Litinin, 13 ga watan Yuli.

Furucin tsohon shugaban kasar ya zo a yayin da ya mayar da martani kan masu cecekucen ya yi watsi ko kuma bai tsinanawa 'yan kabilarsa ta Yarbawa komai ba a lokacin da yake mulki.

Ya ce "babu wata maganar alfarma a lokacin da ya ke jagoranci kuma kowa nasa ne, duk wadanda suka yi aiki tare da shi sun sani kuma za su iya tsaya masa shaida."

"Ban taba fitowa nace banyi kuskure ba a lokacin da nake mulki, amma babu wani abu da nayi da nufin son zuciyata ni kadai sai don ci gaban kasar nan."

KARANTA KUMA: Sarki Bayero ya hana yin kilisa a Kano

"Duk wani kuskure da muka yi, ya auku ne ba niyya ba sai da nufin ganin kasar nan ta bunkasa, amma ba don son kanmu ba."

"Wasu daga cikin 'yan kabilar Yarbawa sun same sun ce ban tsinana musu komai ba."

"Na tambaye su ko na yi wa Najeriya bajinta, sun amsa cewa tabbas na yi. To kuwa matukar na yi wa Najeriya aiki na yi wa dukkanin kabilu."

"Najeriya ba ta Yarbawa ce kadai ba, akwai Inyamurai kuma akwai Hausawa."

Obasanjo ya shawarci gwamnatin mai ci a Najeriya da ta rike tuntubar halin da ake ciki da kuma ababen da ke faruwa a kasar domin sanin madafar da za ta kama wajen sauke nauyi da rataya a wuyanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel