Boko Haram: Sojoji 4 sun mutu, sojoji da fasinjoji sun bace a sabon hari

Boko Haram: Sojoji 4 sun mutu, sojoji da fasinjoji sun bace a sabon hari

Wasu 'yan bindiga da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai wa tawagar sojoji da wasu masu ababen hawa hari, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A take suka kashe sojoji hudu, yayin da mutane da yawa suka bace a karamar hukumar Kaga ta jihar Borno, wata majiya daga jami'an tsaro ta sanar.

An gano cewa maharan sun tare masu ababen hawan a kusa da garin Mainok da ke Kafa wurin karfe 2 na yamma. Sun halaka a kalla rayuka hudu tare da kone ababen hawan sojojin.

Majiyar jami'an tsaron ta ce maharan sun yi awon gaba da makaman sojojin kuma masu tarin yawa har yanzu ba a san inda suke ba.

Kamar yadda majiyar ta kara da cewa, an kone wata motar daukar kaya tare da wata mota kirar Hilux a yayin harin.

"Sun bibiyi tawagar rundunar sojin amma jami'an RRS sun isa inda suka samu gawawwakin sojoji hudu. Abun akwai tashin hankali. Bayan ceton sauran da jami'an suka yi, sun kwato a kalla bindigogi kirar AK 47 guda 7." majiyar tace.

Wata majiya daga 'yan sa kai ta ce harin ya faru ne a kauyen Kongiri kusa da Mainok a kan babbar hanyar Maiduguri kuma fasinjoji da yawa sun bace.

Boko Haram: Sojoji 4 sun mutu, sojoji da fasinjoji sun bace a sabon hari
Boko Haram: Sojoji 4 sun mutu, sojoji da fasinjoji sun bace a sabon hari. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Boko Haram sun yi wa barikin soja 'zobe' a Borno

A wani labari na daban, shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa shi da sauran shugabannin tsaro da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a shekaru biyar da suka gaba basu bashi kunya ba.

Suna kuma yi babban kokari wurin ganin sun sauke nauyinsu da aka dora musu, The Punch ta ruwaito.

Buratai ya yi wannan bayanin ne yayin da ya tarba shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Gabriel Olanisakin bayan da ya kai ziyara sansani na hudu na sojin kasa da ke Faskari a jihar Katsina.

Olanisakin ya kai ziyara sansanin ne don ganin yadda aikin atisayen 'Sahel Sanity' ke tafiya.

Buratai ya ce, "Yanzu shekaru 5 cif kenan da suka gabata. Ina Ndjamena, jamhuriyar Chadi a lokacin da naji sanarwar nadin Janar Olanisakin a matsayin shugaban ma'aikatan tsaro da nawa nadin.

"Muna godiya ga Allah da ya bamu lafiya mai inganci da muke shugabantar jami'an.

"Abun jin dadi ne mu sanar da shugaban kasar cewa muna matukar godiya a kan wannan karamcin kuma muna sake tabbatar da cewa ba za mu bashi kunya ba wurin sauke nauyin da ke kanmu.

"Ba za mu bai wa 'yan Najeriya kunya ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel