Magu: Emmanuel Omale ya na barazanar karar ‘Yan jarida, ya nemi N1bn

Magu: Emmanuel Omale ya na barazanar karar ‘Yan jarida, ya nemi N1bn

- Emmanuel Omale ya na barazanar shigar da karar Naira biliyan 1 a kan NAN

- Faston ya musanya zargin da aka jife sa da shi na sayen gidan miliyoyi a Dubai

- Ana rade-radin cewa Omale ya na da hannu wajen taya Magu satar wasu kudi

Malamin addinin kirista, Emmanuel Omale ya yi magana game da zarginsa da ake yi da hannu wajen sayen wani gida na Naira miliyan 573 da sunan Ibrahim Magu.

Emmanuel Omale ya karyata wannan zargi, ya kuma ce zai iya kai kara gaban kotu ta bakin Lauyansa, Gordy Uche (SAN), ya nemi a biya shi Naira biliyan daya na bata masa suna da aka yi.

Faston ya ce babu shakka ya hadu da Ibrahim Magu kwanakin baya a birnin Dubai a shekarar nan, amma ya ce sam ba batun sayen gida ta hada su ba.

Da ya ke wanke kansa a wasikar da ya aikawa hukumar dillacin labarai na kasa ta bakin babban Lauyan, faston ya ce rashin lafiya ta kai Magu kasar waje, shi kuma ya yi masa addu’a.

A cewar malamin kiristan, rahoton da NAN ta fitar sharri ne da matukar jawo masa cin mutunci da yunkurin goga masa baki a suna, tare da jawo masa bakin jinin jama’a.

KU KARANTA: Ministan shari'a ya na fuskantar barazanar daurin shekaru 5

Magu: Emmanuel Omale ya na barazanar karar ‘Yan jarida, ya nemi N1bn
Wasikar Emmanuel Omale
Asali: Original

Faston ya koka da cewa wannann rahoto zai iya yin sanadiyyar jefa sa a matsala a aikin addinin da ya ke yi a matsayinsa na babban limamin cocin Divine Hand of God Prophetic Ministries International.

A wasikar, Lauyan Omale ya ce: “Za mu yi wa jama’a karin hasken gaskiyar abin da ya faru: wanda mu ke karewa fitaccen limamin babban coci ne.”

“Wanda mu ke karewa ya kai wa Ibrahim Magu ziyara ne a asibiti a Dubai, kasar UAE a cikin Maris 2020.”

“Wanda mu ke karewa bai taba wawurar ko wani irin kudi ga Ibrahim Magu ko wani ba. Ba shi da akawun a bankin kasar waje a ko ina a Duniya."

Uche SAN ya gargadi NAN cewa idan ba su janye rahoton na su ba, faston zai bukaci N1b a hannunsu saboda yunkurin bata masa suna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel