Bayan tube rawaninsa da marigayi Ado yayi, Sarkin Kano zai yi wa Babba-Dan-Agundi sarauta

Bayan tube rawaninsa da marigayi Ado yayi, Sarkin Kano zai yi wa Babba-Dan-Agundi sarauta

Sarkin Kano, Aminu Bayero ya nemi amincewar gwamnatin jihar a kan ya sake nada Aminu Babba Dan Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Maituta kuma hakimin Gabasawa.

Idan za mu tuna, marigayi sarkin Kano, Ado Bayero, ya kwace rawanin Dan Agundi a 2003 sakamakon zarginsa da yayi da rashin biyayya.

Tubabben mai sarautar ya maka Sarkin gaban kotun inda babbar kotu da ta daukaka kara suka bai wa Babba Dan Agundi gaskiya, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Amma kuma, a ranar 5 ga watan Yunin 2020, kotun koli ta murje hukuncin kotu biyun da suka bai wa Dan Agundi gaskiya tare da jaddada tube rawaninsa.

Amma kuma, a wani sabon tsari da ake zargi da hannun gwamnatin jihar, an mayar da Babba Dan-Agundi cikin 'yan majalisar masarautar tare da bashi sabuwar sarautar Sarkin Dawaki Babba.

A wata wasika da aka mika ga sakataren gwamnatin jihar da kuma mataimakin sakataren masarautar, Sarkin na bukatar amincewar gwamnan jihar wurin nada babban yayansa, Sanusi Bayero, a matsayin Wamban Kano.

Bayan tube rawaninsa da marigayi Ado yayi, Sarkin Kano zai yi wa Babba-Dan-Agundi sarauta
Bayan tube rawaninsa da marigayi Ado yayi, Sarkin Kano zai yi wa Babba-Dan-Agundi sarauta. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda na zazzabga wa ministan Buhari mari bayan ya neme ni da lalata - Nunieh

"An umarceni da in sanar da ku cewa, bayan taron masarautar Kano na ranar 8 ga watan Yulin 2020, mun yanke hukuncin bada wadannan sarautun:

"1. Alhaji Sanusi Ado Bayero, tubabben Chiroman Kano za a bashi sarautar Wamban Kano kuma dan majalisar masarautar Kano.

"2. Alhaji Aminu Babba Dan Agundi tubabben Sarkin Dawaki Maituta, za a bashi sarautar Sarkin Dawaki Babba kuma dan majalisar masarautar Kano," cewar takardar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel